Mutane 1,358 ne suka mutu ta dalilin korona a Najeriya

Mutane 1,358 ne suka mutu ta dalilin korona a Najeriya

- Kwayar cutar korona na ci gaba da yaduwa a Najeriya a kowacce rana

- NCDC sun tabbatar da kamuwar mutane 1024 a jihohi 17 a fadin kasar ranar lahadi da ta gabata

- Hukumar ta kuma tabbatar da mutuwan mutane 1,358 daga farkon yaduwar cutar zuwa yau

Cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya ta ce wadanda aka tabbatar da sun kamu da kwayar cutar korona sun haura zuwa 100,087 a kasar, The Punch ta ruwaito.

Wannan na zuwa makonni 45 bayan kasar ta tabbatar samun mutum na farko mai dauke da COVID-19 a ranar 27 ga Fabrairu, 2020, bisa ga bayanan da ke shafin yanar gizon NCDC a ranar Litinin, 11 ga Janairu.

Hukumar ta kuma ce daga cikin adadin 100,087 da suka kamu da cutar COVID-19, an sallami marasa lafiya 80,030 yayin da 1,358 suka mutu.

KU KARANTA: An kama wasu 'yan fashi 2 biyu a jihar Kano

Mutane 1,358 ne suka mutu ta dalilin korona a Najeriya
Mutane 1,358 ne suka mutu ta dalilin korona a Najeriya Hoto: NCDC
Asali: Twitter

Bayanai sun kuma nuna cewa akwai mutane 18,699 da suka kamu da cutar a Najeriya, inda Legas da FCT ke da 6,858 da 5,563 bi da bi.

Bayanai daga shafin yanar gizon NCDC sun kuma bayyana cewa kasar ta samu sabbin kamuwa da cutar 1,024 a cikin jihohi 16 da Babban Birnin Tarayya a ranar 10 ga Janairun 2020.

Hukumar ta NCDC ta ce, “A ranar 10 ga watan Janairun 2021, an tabbatar da sabbin kamuwa da cutar 1024 da kuma mutuwar mutane 8 a Nijeriya.

“Har zuwa yau, an tabbatar da kamuwa da cutar 100087, an saki wadanda suka kamu da cutar 80030, an kuma samu mutuwar mutane 1358 a cikin jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya.

“An samu rahoton sabbin kamuwa da cutar 1024 daga jihohi 17- Lagos (653), Plateau (63), Benue (48), Zamfara (45), FCT (42), Rivers (27), Ondo (26), Adamawa (26) , Kaduna (22), Edo (18), Ogun (16), Imo (12), Kano (9), Yobe (6), Ekiti (5), Jigawa (4) da Osun (2).

KU KARANTA: Ana bukatar 'yan sandan jiha don yaki da ta'addanci - Akeredolu

"Cibiyar ayyukan gaggawa ta bangarori daban-daban, da aka nada a Mataki na 3, na ci gaba da daidaita ayyukan daukan mataki ga kasa."

A wani labarin, Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa ta yi karin haske kan cewa allurar rigakafin kwayar cutar korona da Gwamnatin Tarayya za ta sayo ba ta dauke da fasahar tattara bayanai (microchips).

Hukumar ta fadi haka ne a cikin jerin sakonnin tweets mai taken ‘Abubuwan da ya kamata a sani game da allurar rigakafin # COVID19!’ A ranar Lahadi.

Akan ko allurar rigakafin ta COVID-19 ta ƙunshi fasahar tattara bayanai (microchip), hukumar Gwamnatin Tarayya ta ce Ma’aikatar Kiwon Lafiya za ta tabbatar da allurar rigakafin kafin a yi ta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel