Nyesom Wike Ya Sake Fallasa Abin da Wasu daga cikin Gwamnoni Suka Yi Masa
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya zargi wasu gwamnoni da haddasa rikicinsa da Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, yana mai cewa yanzu sun sasanta
- Wike ya ce Fubara yana farin cikin tallafa wa Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa sun yafewa juna kuma sun sake haɗa kan danginsu na siyasa
- Da aka tambaye shi ko yana shirin bai wa Fubara muƙamin minista bayan barin mulki, Wike ya ce shugaban ƙasa ne kaɗai ke da ikon naɗa ministoci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya zargi wasu gwamnoni da haddasa rikicin siyasa a Rivers.
Wike ya ce wasu na haddasa rigima tsakaninsa da Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, yana mai cewa yanzu suna aiki tare, kuma yan yana farin cikin yi wa Bola Tinubu aiki.

Source: Facebook
Haan na cikin wata zantawa yayin da yake magana a taron ganawa da manema labarai na wata-wata a Abuja ranar Talata, cewar Punch.
Wike ya tuna gudunmawar da ya ba Gwamna
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana yadda ya yi aiki da jam’iyyarsa ta PDP domin taimaka wa Monday Okpebholo na APC.
Wike ya ce ya ƙi goyon bayan Asue Ighodalo duk da cancantarsa, saboda bai son tsohon gwamna Godwin Obaseki ya sake samun iko.
Ya bayyana cewa ƙungiyar Rainbow Coalition za ta haɗa kan ’yan APC da PDP domin tallafa wa Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Abin da ya fi muhimmanci a siyasa - Wike
Wike ya ce abin da ya fi muhimmanci shi ne tabbatar da cewa bangaren siyasar Fubara sun kasance cikin haɗin kai, ko da kuwa zai sake tsayawa takara ko a’a.
Ya ce mutanen da ba su yi wa gwamnan fatan alheri ba ne suka haddasa matsalolin da suka faru.
Wike ya ce:
“Dukkanmu mun zama ɗaya, mun yafewa juna, kuma mun sake haɗuwa. Amma gaskiya tana nan daram.”
Ya nuna cewa “munanan ayyukan wasu ’yan Najeriya” ne suka jawo rikicin amma a yanzu an samu maslaha.

Source: Facebook
Wike ya ce Fubara ba ya tallafa wa kamfen ɗin shugaban ƙasa ba tare da son ransa ba.
Ya tambaya:
“Yana farin ciki da rawar da muke ba shi. Idan ba ya farin ciki, me ya sa za ku shirya taro a gidansa? Kun san abin da ake buƙata kafin a shirya taro a gidansa, inda kowa zai halarta?”
Da aka tambaye shi ko yana shirin samar wa Fubara muƙamin minista bayan ya bar mulki a shekara mai zuwa, Wike ya ce ba shi ne ke da ikon yanke wannan shawara ba.
Ya ce:
“Ni ba shugaban ƙasa ba ne da zan zaɓi wanda zai zama minista. Ba ni da ikon gabatar da sunan kowa domin naɗin minista.”

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Ministan Tinubu ya ɓallo magana kan takarar Sheikh Pantami a zaben 2027
Kalaman Wike ga yan takarar PDP
Kun ji cewa Angulu Bako, Gomna Stephen Gashe da Ahmed Dogara Jacob sun yafe takarar majalisa da suka samu a Abuja.
‘Yan takaran na PDP sun shaida wa kowa cewa sun fasa shiga zabe kuma jam’iyyar APC za su yi wa aiki a 2027.
Nyesom Wike ya jagoranci wannan yunkuri domin a kara wa APC da Bola Tinubu karfi a babban birnin tarayya.
Asali: Legit.ng

