Tsaro Ya Lalace: ’Yan Bindiga Sun Sace Kansila da ’Ya’yansa 2 a Kaduna
- Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun yi garkuwa da kansilan Zaria mai kula da ayyuka na musamman tare da ’ya’yansa biyu.
- Lamarin ya faru da tsakar dare a unguwar Wucicciri, yankin Abba, inda maharan suka kutsa gidan kansilan
- Yankin ya daɗe yana fama da satar mutane da shanu, yayin da ƙoƙarin jin ta bakin ’yan sanda da hukumomin ƙaramar hukumar bai yi nasara ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Zaria, Kaduna - Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun yi garkuwa da wani kansila mai kula da ayyuka na musamman a Ƙaramar Hukumar Zaria ta Jihar Kaduna.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an sace Lamido Muhammad ne tare da ’ya’yansa biyu, Aliyu Lamido da Amir Lamido yayin harin.

Source: Original
Kaduna: Yadda aka sace kansila da 'ya'yansa
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12 na dare ranar Lahadi, lokacin da maharan suka kutsa gidan kansilan da ke unguwar Wucicciri, a yankin Abba na ƙaramar hukumar, cewar Aminiya.
Majiyoyi sun ce maharan sun tafi da jami’in da ’ya’yansa zuwa wani wuri da har yanzu ba a san inda yake ba.
Kansilan wanda ɗan asalin ƙauyen Kaladi da ke gundumar Wucicciri ne, tsohon malamin makaranta ne kafin ya shiga harkokin siyasa, inda daga baya ya zama kansila mai kula da ayyuka na musamman a ƙaramar hukumar.
Wata majiya ta bayyana cewa kansilan na daga cikin mutanen da ke ba da gudummawa wajen ci gaban al’ummarsa.
Ta ƙara da cewa ana sa ran zai kasance cikin waɗanda za su gudanar da aikin Hajjin bana.
Sace kansilan da ’ya’yansa ya faru ne a yankin da ya daɗe yana fama da matsalolin tsaro, musamman satar mutane da satar shanu.
Bayanai sun nuna cewa ƙauyukan Kaladi da Yaskwake, da kuma unguwannin Zakarar Mahauta da Zakarar Fulani, sun fuskanci hare-haren ’yan bindiga a shekarun baya.

Source: Facebook
Yadda yan bindiga suna addabi kansilan Zaria

Kara karanta wannan
Kakar miliyoyin matasa ta yanke saƙa, an fadada shirin tallafin rage talauci a Najeriya
Majiyar ta ce a shekarar da ta gabata ma, Lamido yana cikin mutanen da ’yan bindiga suka sace wa shanunsu yayin wani hari da suka kai ƙauyensu.
Majiyoyi suka ce yan jarida sun ziyarci ofishin Ƙaramar Hukumar Zaria domin samun ƙarin bayani kan lamarin, amma bai samu wani jami’i da zai yi magana a hukumance ba.
Haka kuma, ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, DSP Mansur Hassan, bai yi nasara ba, duk da kiraye-kirayen waya da saƙonnin tes da aka aike masa.
An kashe dan bindiga, Wakiyu a Katsina
Mun ba ku labarin cewa Jami'an tsaro sun yi nasarar kawo ƙarshen daya daga cikin harsabiban yan bindiga a jihar Katsina da ke Arewa maso Yamma.
An kashe wani fitaccen dan bindigan ne yayin arangama tsakanin sojoji, ’yan sanda da jami’an C-Watch a Katsina da ke fama da matsalar tsaro.
Rahotanni sun ce marigayin na da alaƙa da ƙungiyar Kachalla Maha, kuma ana zarginsa da addabar mazauna Matazu da makwabtansu.
Asali: Legit.ng
