Kwana Ya Kare: Fitaccen Mawakin Addini a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Shahararren mawaƙin waƙoƙin addinin Kirista a Najeriya, Olayemi Bolaji, wanda aka fi sani da Toluwanisings, ya riga mu gidan gaskiya
- Rrahotanni sun nuna cewa mawaƙin ya rasu ne da sanyin safiyar Laraba, 14 ga Oktoba, 2026, kamar yadda iyalansa suka bayyana a cikin wata sanarwa da suka fitar
- Labarin rasuwarsa ya jawo jimami daga masoyansa, abokan sana'arsa da sauran fitattun mutane a kafafen sada zumunta, inda aka fara tura sakonnin ta'aziyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ibadan, jihar Oyo - Shahararren mawaƙin addinin Kirista a Najeriya, Olayemi Bolaji, wanda aka fi sani da Toluwanisings, ya riga mu gidan gaskiya.
Bayanan da suka fito zuwa yanzu sun nuna cewa mawaƙin ya rasu ne da sanyin safiyar Laraba, 14 ga Oktoba, 2026.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa iyalansa ne suka tabbatar da rasuwar mawakin a cikin wata sanarwa da suka fitar.
An sanar da rasuwar Toluwanisings
A cikin sanarwar, iyalan sun bayyana shi da sunan Minista Olayemi Bayonile Bolaji na ma'aikatar waƙoƙin addinin Kirista ta Toluwani Gospel Music Ministry (TOGOMM).
Sanawar ta kuma bayyana marigayin a matsayin miji ƙaunatacce, ɗan uwa kuma mai wa'azin bishara ta hanyar waƙa ga mabiya addinin kirista a fadin kasar nan.
Sanarwar ta ce:
“Cikin tsananin alhini, iyalai suna sanar da rasuwar Minista Olayemi Bayonile Bolaji na ma'aikatar wakokin addinin Kiritsa ta Toluwani Gospel Music Ministry (TOGOMM), wanda ya rasu da sanyin safiyar ranar 14 ga Oktoba, 2026.
“Ya kasance miji da muke kaunwa, ɗan uwa kuma mai wa'azin bishara ta hanyar waƙa ga mabiya addinin Kirista.
“Muna roƙon ku da ku riƙa sanya matarsa, iyalansa da sauran masoyansa cikin addu'o'inku a wannan lokaci mai wuya.”
Sanarwar da Iyalan mamacin suka fitar ta ƙara da cewa za su sanar da jama'a bayanan shirye-shiryen jana'izarsa nan gaba.

Kara karanta wannan
Dalla dalla: Yadda za ka duba wayarka ta cika sharaɗin NCC domin kada a rufe maka ita
Masoya sun fara alhinin rasuwarsa
Labarin rasuwarsa ya jawo jimami daga masoyansa, abokan sana'arsa da sauran fitattun mutane a kafafen sada zumunta, inda da dama suka yi alhinin rashin mawaƙin.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a bayyana musabbabin rasuwar Toluwanisings ba, sai dai tuni iyalansa suka fara karbar sakonnin ta'aziyya daga mutane daban-daban.

Source: Instagram
Leadership ta ruwaito cewa mawakin ya fito ne daga jihar Osun, kodayake ya kuma gina masu sauraron wakoki a Ibadan, jihar Oyo, inda aka lissafa shi a matsayin wanda ya yi fice a wakokin yabo na Kirista.
Farfesa Sobowale ya mutu
A wani labarin, kun ji cewa masanin sadarwa kuma jigo a fannin yaɗa labarai da sadarwa a Najeriya, Farfesa Idowu Akanbi Sobowale, ya rasu yana da shekara 85.
Dan uwan mamacin, Sowunmi ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga al’ummar fannin sadarwa, musamman mambobin kungiyar masa da kwararrun sadarwa ta Najeriya.
Ayyukan farko da Farfesa Sobowale ya yi, da sauran gudunmawarsa, sun sa gwamnatin Cif Olusegun Obasanjo ta ba shi lambar yabo ta ƙasa ta (OON) a lokacin Jamhuriyya ta Hudu.
Asali: Legit.ng
