Dalla Dalla: Yadda Za Ka Duba Wayarka Ta Cika Sharadin NCC domin Kada a Rufe Maka Ita
Abuja, Nigeria - Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta bullo da wani tsari domin tangance wayoyi, kwamfutoci da sauran nau'ikan na'urorin da ake sanya wa layin SIM.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
A karkashin wannan tsari, NCC ta nuna yadda ’yan Najeriya za su iya tantance ko ta amince da wayoyinsu domin amfani da su a hanyoyin sadarwar kasar nan.

Source: Getty Images
Tashar Channels tv ta ruwaito cewa duk wayar da ta gaza tsallake wannan mataki na tamtncewa, NCC za ta sauke ta daga hanyoyin sadarwa a Najeriya ma'ana za ta daina aiki.
NCC ta bullo da tsarin tantancewa
Hukumar ta bayyana cewa wannan mataki na cikin sabon tsarin tabbatar da bin ƙa’idojin amincewa da na’urori, wanda ya fara aiki a ranar 7 ga Oktoba, 2026.
Manufar tsarin ita ce kare masu amfani da wayoyi, tabbatar da tsaron hanyoyin sadarwa da kuma tabbatar da cewa na’urorin da ake sayarwa da amfani da su a Najeriya sun cika ƙa’idojin fasaha da aka gindaya.

Kara karanta wannan
NCC ta ɓullo da wani tsari, mutane na iya asarar wayoyin da suka Ssaya da kuɗinsu a Najeriya
Daraktan Ƙa’idojin Fasaha da Ingancin Hanyoyin Sadarwa na hukumar, Edoyemi Ogoh, ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai wanda aka gudanar a Abuja ranar Talata, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Idan kana da waya, ko kana shirin sayen sabuwar waya ko wadda aka yi amfani da ita a baya, ga yadda za ka tantance matsayinta kafin ka biya kuɗi.
Yadda za ka tantance wayarka
Bi waɗannan matakai domin tabbatar da matsayin wayarka:
Mataki na 1: Danna *315#
Buɗe wajen buga lambobi a wayarka, sannan ka danna *315# domin shiga tsarin tantance na’urori na NCC. Bi umarnin da zai bayyana a allon wayarka.
Mataki na 2: Ziyarci shafin NCC
Haka kuma, za ka iya ziyartar shafin hukumar ta intanet ta wannan adireshi: www.ncc.gov.ng/devicechecker domin amfani da tsarin tantance na’urori.
Mataki na 3: Nemo lambar IMEI
Idan kana son tantance wata waya daban da wadda kake amfani da ita, za ka iya buƙatar lambar IMEI mai lambobi 15, wato lambar tantance na’urar sadarwa ta wayar hannu.
Domin samun lambar, danna *#06# a wayar. Lambar IMEI za ta bayyana a allon wayar.
Idan wayar da kake son saya ce, ka nemi mai sayar da ita ya ba ka damar amfani da wayar domin gano lambar IMEI ɗinta da kammala tantancewa.

Source: Getty Images
Mataki na 4: Bi umarnin tantancewa
Shigar da bayanan da ake buƙata, sannan ka bi umarnin da tsarin tantancewar ya bayar domin gano matsayin na’urar a wurin hukumar NCC.
Mataki na 5: Duba sakamakon
Ka duba bayanan da tsarin ya nuna kafin ka sayi wayar. Idan ba ka fahimci matsayin na’urar ba ko kuma tantancewar ta gaza, ka nemi ƙarin bayani daga mai sayar da wayar ko NCC kafin ka kammala cinikin.
Rashin samun nasarar tantance waya ba yana nufin cewa lallai jabun waya ce ba. Ana iya buƙatar ƙarin bincike domin tabbatar da ko ta cika ƙa’idojin da ake buƙata.
Dole ne tantance wayoyin da ake amfani da su?
A cewar NCC, an riga tantance wayoyin da tuni suke amfani hanyoyin sadarwar wayoyin hannu na Najeriya kafin fara aiki da sabon tsarin ta atomatik.
Saboda haka, galibi masu amfani da irin waɗannan wayoyi ba sa buƙatar ɗaukar wani mataki.

Kara karanta wannan
Abu ya yi kyau: An ƙara wa 'yan Najeriya damar sayen hannun jari a matatar Dangote
Sai dai hukumar ta shawarci masu sayen wayoyin hannu da aka yi amfani da su a baya, da kuma na’urorin da ba su taɓa haɗuwa da wata hanyar sadarwa ta Najeriya ba, da su tantance matsayinsu kafin kammala saye.
Za a dauki yan soshiyal midiya aiki
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta shirya ɗaukar yan soshiyal midiya 4,000 msu karfin mabiya a kafafen sada zumunta domin tallata ayyukan Shugaba Tinubu.
Ministan Ayyuka, David Umahi ya ce za a yi amfani da yan midiya wajen isarwa da bayanan ayyukan gwamnati ga ’yan Najeriya, musamman matasa
Asali: Legit.ng
