Ana bukatar 'yan sandan jiha don yaki da ta'addanci - Akeredolu

Ana bukatar 'yan sandan jiha don yaki da ta'addanci - Akeredolu

- Gwamnan jihar Ondo ya yabawa sojoji tare da karfafa bukatar samun 'yan sandan jihohi

- Gwamnan ya gabatar da jawabinsa ne a yayin bikin tunawa da sojoji na 2021

- Birigediya Kwamanda Zakari Abubakar ya yabawa gwamnan da sadaukarwarsa akan sojoji

Gwamnan jihar Ondo, Mista Rotimi Akeredolu, ya yi kira da a samar da tsarin ‘yan sanda mai matakai daban-daban, yana mai cewa ita ce hanya mafi kyau da za ta fitar da kasar daga matsalar tsaro da take fuskanta a‘ yan kwanakin nan, The Punch ta ruwaito.

Gwamnan ya kuma jaddada cewa batun ‘yan sandan jihohi ya zama dole a yanzu fiye da kowane lokaci.

Akeredolu ya bayyana hakan ne a wurin hidimar kirista na jihar don tunawa da ranar da Sojoji na 2021, wanda aka yi a cocin Katolika na St. Benedict, Owena Cantonment na sojojin Najeriya, kan hanyar Onda, Akure, ranar Lahadi.

KU KURANTA: APC tayi tir da tarzomar Amurka, ta roki Trump da yayi koyi da Buhari

Ana bukatar 'yan sandan jiha don yaki da ta'addanci - Akeredolu
Ana bukatar 'yan sandan jiha don yaki da ta'addanci - Akeredolu Hoto: Naira Metrics
Asali: UGC

Gwamnan ya kuma ce akwai bukatar kara samar da kayayyakin aiki na zamani ga sojojin Najeriya don taimakawa a yakin da suke yi da masu tayar da kayar baya da sauran laifuka a kasar.

Ya bayyana cewa samar da "mafi kyawun harsashi da jin dadin hukumomin tsaro dole ne su ci gaba da kasancewa a kan gaba, don kara karfafa gwiwa da tallafawa jami'an a yakin da suke yi da aikata laifuka."

Ya yaba tare da nuna goyon baya da jajircewar sojoji wajen tabbatar da tsaro a jihar da kuma tunkarar masu satar mutane da sauran masu aikata laifuka wadanda ke kawo zaman lafiya a jihar,.

Gwamnan ya ce kokarin da sojojin Najeriya ke yi na yaki da ta'addanci da nufin kare kasar nan da kuma kawar da masu aikata laifuka abin yabo ne.

KU KARANTA: Sojoji Sun Kashe Sama Da 'Yan Bindiga 50, Sun Kwato Dabbobin Da Aka Sace A Zamfara

A nasa jawabin, Birged Kwamandan na 32 Artillery Brigade, Zakari Abubakar, ya yaba da sadaukarwar Akeredolu ga rundunar, sojoji, zawarawa, da kuma masu dogaro da wadanda suka mutu.

Ya ce rundunar ta amince tare da kimanta ci gaba da goyon baya da karfafa gwiwa da gwamnan yake ba su, inda ya bukace shi da ya ci gaba da tallafawa sojojin.

A wani labarin daban, An samu barkewar rikici a jihar Oyo ranar Asabar kan kisan wasu Fulani uku, da suka hada da uba da ‘ya’yansa maza guda biyu, da kungiyar tsaro ta Kudu maso Yamma, Amotekun ta aikata.

An kashe Alhaji Usman Okebi tare da ‘ya’yansa a lokacin da jami’an Amotekun suka afka wa matsugunan Fulani a Okebi da ke karamar hukumar Ibarapa ta Arewa.

Wannan lamarin shine mafi sabani a cikin jerin keta, take hakki da kuma nuna kyama ta sabuwar kungiyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.