ASUU na neman garantin kariya kan sake bude makarantu

ASUU na neman garantin kariya kan sake bude makarantu

- Kungiyar malaman jami'a ta bukaci gwamnati ta basu tabbacin tsaro daga COVID-19 kafin su koma

- Kungiyar ta koka da nuna shakku kan binciken da wasu cibiyoyi suka gudanar

- Hakazalika kungiyar ta bayyana shirin ta da mambobinta kan dawowa kan aiki

Malaman jami’a a ranar Litinin sun bayyana shirye-shiryensu na ci gaba da harkokin karatunsu a ranar Litinin mai zuwa kamar yadda Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ta umurce su, The Nation ta ruwaito.

Malaman, sun roki Gwamnatin Tarayya da ta tabbatar musu da lafiyar su da ta daliban su a yayin da ake kokarin shawo kan cutar ta COVID-19.

Shugaban Kungiyar Malaman Jami'o'in (ASUU), Farfesa Biodun Ogunyemi, ya ce tantancewar da rassanta suka yi ya nuna cewa mahukuntan jami'ar ba su yi abin da ya kamata ba don tabbatar da yanayin koyo mai inganci.

KU KARANTA: An daure wani mai wa'azi a Turkiyya shekaru 1,000

ASUU na neman garantin kariya kan sake bude makarantu
ASUU na neman garantin kariya kan sake bude makarantu Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Ya ce: “Ba mu da wata adawa game da batun dawowar jami’o’i. ASUU ta dakatar da yajin aikin da take yi kuma membobinmu a shirye suke su yi aiki.

“Duk da haka, dole ne a tabbatar da lafiya da amincin membobinmu har ma da dalibanmu.

“Ina fatan gwamnati za ta yi aiki tare tare da hukumomin jami’o'i don tabbatar da cewa wannan karo na biyu na COVID-19 bai shafi lafiya da amincin al’ummomin jami’ar ba."

Shugaban kungiyar ya kirayi gwamnati da ta kimanta ta yi yadda tayi a tashoshin jirgin sama don inganta lafiya da kiyayewa.

KU KARANTA: Wani dan majalisa zai tallafawa Almajirai da kudi N200m

Ya kuma yi kira cewa: "ya kamata su kimanta matakin shirye-shirye kuma su fada wa‘ yan Najeriya cewa da abin da suka gani za su iya tabbatar da cewa idan daliban suka dawo, idan malamai suna da darasi, za a samu babu wani mummunan sakamako.”

A wani labarin, Najeriya a halin yanzu tana da karancin malamai 277,537 a cewar rahoton binciken ma'aikata na kasa na shekarar 2018 kan Makarantun Ilimin na Gwamnati da Masu zaman kansu a Najeriya, The Punch ta ruwaito.

Binciken na ma'aikata wanda Hukumar Kula da Ilimin Farko ta Kasa ta nuna ya nuna cewa "yayin da 73% na wadanda ke koyarwa a makarantun gwamnati kwararrun malamai ne, kashi 53 cikin 100 na malamai a makarantu masu zaman kansu ne suka cancanci koyarwa."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.