Bankole zai auri diyar gwamnan jihar Kebbi
- Tsohon kakakin majalisa zai angwance da diyar gwamnan jihar Kebbi
- An sanya ranar daurin aurensu 15 ga watan Janairun wannan shekara
- Masu sharhi a siyasa sun lura cewa auren zai jawo tsegumi tsakanin APC da PDP
Wani tsohon kakakin majalisar wakilai Dimeji Bankole a ranar Juma'a 15 ga watan Janairu zai angwance da Aisha Shinkafi Saidu, diyar gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, The Nation ta ruwaito.
Bankole, wanda ya rabu da matar sa ta farko a shekarar 2017, ya kasance mai matukar neman haihuwa cikin rukunin wadanda suka cancanta a ciki da wajen Najeriya.
Bikin auren na ranar Juma’a zai jawo labule kan jita-jita dangane da niyyar aurensa tun bayan sakin.
Amaryar, lauya ce da ta ta kammala karatun ta a Jami'ar Hull a Biritaniya kuma jikanyar marigayi Alhaji Umaru Shinkafi, Marafan Sokoto ne, babban dan siyasa kuma tsohon shugaban kungiyar tsaro ta Najeriya.
KU KARANTA: Pat Utomi ya siffanta 'yan siyasar arewa da cimma zaune
Mahaifiyar amaryar ‘yar Shinkafi ce kuma kanwa ga tsohon Gwamnan Zamfara, Aliyu Shinkafi.
Wata sanarwa daga dangin Bankole na Iporo, Abeokuta ta bayyana cewa an gabatar da wata tattaunawa tsakanin iyayen biyu don fara haduwa kamar yadda addinin Musulunci da umarnin gargajiya suka tanada.
A taron gabatarwar, Gwamnan Sakkwato kuma magajin Bankole a matsayin Shugaban Majalisar Wakilai, Aminu Tambuwal, ya jagoranci dangin ango zuwa gidan dangin amarya don neman aurenta.
KU KARANTA: 'Yan sanda sun kame wasu Fulani 47 dauke da makamai a Oyo
Masu lura da al'amuran siyasa duk da haka sun lura cewa auren zai bayyana kamar zai kawo cikas ga babban rarrabuwar kawuna a siyasan Najeriya kasancewar Bagudu shine Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC yayin da Tambuwal shine Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP na kasa.
A wani labari daban, Wani dan majalisa, mai wakiltar Bodinga-Dange, a mazabar tarayya ta Shuni-Tureta, Dr. Balarabe Kakale ya ware naira miliyan 200 domin karfafawa Almajiri da kananan ‘yan kasuwa a mazabar sa, Daily Trust ta ruwaito.
A wata hira da aka yi da shi jim kadan bayan rarraba motoci tara, babura 33, kekunan dinki 60, injunan nika 40 da sauransu ga wadanda suka fara cin gajiyar shirin, ya ce an yi hakan ne domin a hana Almajirai yin bara.
Ya kara da cewa yana harin tallafawa almajirai 1000 ne a wannan shekarar kadai, ya kara da cewa shirin zai ci gaba ne
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng