An Kai Ɗan Najeriya Kotu kan Ikirarin Mallaka da Shirin Cefanar da Jirgin Sojoji

An Kai Ɗan Najeriya Kotu kan Ikirarin Mallaka da Shirin Cefanar da Jirgin Sojoji

  • Rundunar ’yan sandan filin jirgin sama ta gurfanar da wani mutum a gaban kotu bisa zargin yin sojan gona
  • Ana zargin shi da wallafa bidiyo a kafar sada zumunta, inda ya yi ikirarin mallakar jiragen yaƙi masu saukar ungulu guda biyu, tare da neman mai saya
  • Kwamishinar ’yan sanda, Olufunke Ogunbode, ta ce lamarin na da barazana ga tsaro, inda ta bukaci kamfanoni su inganta binciken ma’aikatansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Rundunar ’yan sandan filin jirgin sama ta gurfanar da wani mutum mai shekaru 47, Mark Agbor, a gaban kotu.

An gurfanar da mutumin ne bisa zargin yin sojan gona da shiga wuraren sirri ba tare da izini ba a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Lagos.

Kara karanta wannan

Tsaro ya lalace: 'Yan bindiga sun sace kansila da 'ya'yansa 2 a Kaduna

An maka dan Najeriya a kotu kan sayar da jirgin saman sojoji
Jirgi mai saukar ungulu yana shawagi a sararin samaniya. Hoto: Nigeria Air force.
Source: Getty Images

Ana zargin mutumin da wallafa wani bidiyo a kafar sada zumunta, inda ya yi ikirarin cewa shi ne mamallakin jiragen yaƙi masu saukar ungulu guda biyu, tare da bayyana aniyarsa ta sayar da ɗaya daga cikinsu, cewar The Guardian.

An dage shari'ar zuwa watan Nuwamba

An ɗage sauraron karar zuwa ranar 18 ga Nuwamba, 2026 domin tabbatar da yin adalci a shari'ar da ake yi.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan filin jirgin sama, Adeola Mohammed, ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar jiya cewa an miƙa Agbor ga sashen bincike na ƙasa da ƙasa na rundunar domin gudanar da bincike da ɗaukar matakan da suka dace.

An miƙa wanda ake zargin ga rundunar ne daga sashen bincike na rundunar sojojin saman Najeriya da ke Ikeja.

A cewar ’yan sanda, bincike ya nuna cewa wanda ake zargin ya wallafa bidiyon ne a ranar 7 ga Oktoba, 2026, inda ya gabatar da kansa a matsayin mamallakin jiragen yaƙi masu saukar ungulu guda biyu.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda ruwan sama ya ruguza allon tallata Tinubu

Rahoton ya ce Agbor ya kuma bayyana aniyarsa ta sayar da ɗaya daga cikin jiragen, tare da neman mutanen da za su saya.

Dan Najeriya ya saka jiragen sojoji 2 a kasuwa
Taswirar jihar Lagos da ke Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Bayan kammala bincike, rundunar ’yan sandan ta gurfanar da shi a gaban wata kotu mai hurumin sauraron irin wannan shari’a.

Kwamishinar yan sanda ta yi takaici

Kwamishinar rundunar yan sandan filin jirgin sama, Olufunke Ogunbode, ta ce zargin aikata irin wannan laifi na da matuƙar illa ga tsaro, kuma yana iya kawo cikas ga ayyukan hukumomin tsaro.

Ta tabbatar wa jama’a cewa za a bi diddigin lamarin bisa tanadin doka, tare da yabawa rundunar sojojin saman Najeriya bisa haɗin gwiwar da take yi da ’yan sandan.

Ogunbode ta ce wannan shari’a ta nuna muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro wajen magance duk wata barazana da za ta iya shafar tsaron filin jirgin sama, cewar Daily Post.

Ta kuma bukaci kamfanoni da sauran masu ruwa da tsaki da ke gudanar da ayyukansu a filin jirgin sama su ƙarfafa tantance ma’aikata, binciken tarihinsu da tabbatar da sahihancin bayanansu domin rage yiwuwar samun matsalolin tsaro.

Kara karanta wannan

Bayan hana su taro, 'yan Tinubu Must sun yi wa 'yan sanda tambaya 9 masu zafi

Jirgin shugaban Najeriya ya yi kwantai

Mun ba ku labarin cewa jirgin fadar shugaban kasa kirar Boeing 737-700 da aka saka a kasuwa tun watan Yuli, 2025, bai samu mai saye ba har yanzu.

Kamfanin JetHQ na Amurka, wanda ke da alhakin tallata jirgin, ya tabbatar cewa har yanzu jirgin yana nan a kasuwa.

Za a sayar da jirgin ne bayan gwamnatin Bola Tinubu ta fara tsarin rage kashe kudi da kuma rage yawan jiragen shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.