Shekarau Ya Fito da Sabuwar Tafiyar Hada Kuri'un Arewa ga Tinubu a 2027

Shekarau Ya Fito da Sabuwar Tafiyar Hada Kuri'un Arewa ga Tinubu a 2027

  • Sanata Ibrahim Shekarau ya sha alwashin tattara ƙuri’un masu zaɓe a jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya, Abuja, domin tabbatar da nasarar Bola Tinubu a zaɓen 2027
  • Shekarau, wanda ke jagorantar kwamitin amintattu na ƙungiyar Arewa for Asiwaju (A4A), ya bayyana cewa ƙungiyar za ta haɗa kai da jam’iyyar APC wajen ƙara yawan masu kaɗa ƙuri’a
  • Shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya yaba wa ƙungiyar, yana mai cewa haɗin kan manyan ‘yan siyasar Arewa da ke cikinta ya ƙaryata ikirarin cewa yankin ba ya goyon bayan Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma ƙwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Yayin da siyasar zaɓen 2027 ke ƙara ɗaukar zafi, manyan ‘yan siyasar Arewa ƙarƙashin ƙungiyar Arewa for Asiwaju (A4A) sun sha alwashin tattara masu zaɓe a faɗin jihohin Arewa 19 da Abuja.

Kara karanta wannan

Magana ta fito daga bakin minista, an ji adadin shekarun da Tinubu ke buƙata a kan mulki

Tawagar, ƙarƙashin jagorancin Sanata Ibrahim Shekarau da tsohon gwamnan Filato, Simon Lalong, ta gana da shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja.

Kashim Shettima da Ibrahim Shekarau
Ibrahim Shekarau na gaisawa da Kashim Shettima. Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Shekarau ya bayyana cewa an kafa ƙungiyar ne domin ƙarfafa tsarin APC ta hanyar amfani da gogewar tsofaffin gwamnoni, ‘yan majalisa da ƙwararrun masu dabarun siyasa wajen ƙara yawan masu kaɗa ƙuri’a a Arewa.

Yadda A4A ke shirin tara ƙuri’u

Daily Trust ta wallafa cewa shekarau ya ce Arewa ce yankin da ke da mafi yawan masu zaɓe a Najeriya, saboda haka ƙungiyar ta sa a gaba tabbatar da cewa yawan waɗanda za su fito kaɗa ƙuri’a a zaɓen 2027 ya zarce na zaɓukan baya.

Ya bayyana cewa ƙungiyar ta kafa daraktoci sama da 20 masu gudanar da ayyuka, tare da naɗa masu kula da harkokinta a dukkan jihohi, ƙananan hukumomi da mazaɓu.

Shekarau ya ce ƙungiyar ta kuma tattara bayanai kan ayyukan gine-gine da manufofin gwamnatin Tinubu a yankin Arewa domin mayar da martani ga masu zargin cewa gwamnatin ta yi watsi da yankin.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi sabon bidiyo ya kira Tinubu da 'Bola' duk da APC ta yi gargadi

Ya ce:

“Abin da muke yi shi ne ƙara wa APC armashi, domin ita ce babbar jam’iyya. Mun san yawan masu zaɓe a Arewa, wanda ya fi na kowane yanki a ƙasar nan. Burinmu shi ne tabbatar da cewa yawan masu fitowa zaɓe ba kawai ya maimaitu ba, har ma ya ƙaru sosai idan aka kwatanta da zaɓukan baya.”
Motocin Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Motocin tallata Bola Tinubu a Arewa. Hoto: Gov Abdullahi A Sule.
Source: Facebook

A4A za ta ƙaddamar da ofis

Shekarau ya gayyaci shugabannin APC zuwa bikin buɗe sabon ofishin gudanar da ayyukan ƙungiyar da ke Abuja, wanda aka tsara gudanarwa ranar Asabar, 17 ga Oktoba.

Ya tabbatar da cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne zai jagoranci bikin ƙaddamar da ofishin.

Premium Times ta rahoto cewa tsohon gwamnan Filato, Simon Lalong, ya bayyana A4A a matsayin wata rundunar ƙwararrun ‘yan siyasa da ke aiki tare da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ta APC.

Kiran Shettima ga 'yan Arewa

A wani labarin, mun ruwaito cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya fara sabon kamfen domin samun ƙarin goyon bayan Arewa ga ƙoƙarin Tinubu na tazarce a 2027.

Kara karanta wannan

Shettima ya magantu a kan tsoron da 'yan Arewa ke ji a tazarcen Tinubu

Shettima ya tabbatar wa yankin cewa babu abin da zai sa ya ji tsoron sake zaɓen Tinubu, yana mai cewa Arewa za ta ƙara cin moriyar manufofin gwamnatin idan shugaban ƙasar ya samu wa’adi na biyu.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi tawagar ƙungiyar A4A a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a makon nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng