Gwamna Ya Samu Kan Sa a Matsala da Jam’iyyarsa da Aka Cusa Shi a Kamfen Tinubu
- Wasu shugabannin jam’iyyar Accord sun bukaci Gwamna Ademola Adeleke ya fayyace masu matsayinsa
- Hakan ya biyo bayan jin rahoton nada shi jagoran kamfen din Bola Tinubu a Osun duk da bai cikin APC
- Sun ce matakin na iya raunana jam’iyyar tare da rage damar ‘yan takararta da za a shiga zaben 2027 da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Lagos - Wasu shugabannin jam’iyyar Accord sun bukaci Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya fayyace matsayinsa na siyasa.
Hakan ya zama dole ne da aka ji an nada shi jagoran kamfen din sake zaben Shugaba Bola Tinubu a jihar Osun duk da bai cikin APC.

Source: Twitter
Wasikar shugabannin Accord ga Gwamna Ademola Adeleke
Punch ta rahoto Shugabannin Accord a Kudu, Oke Sewedo da Oladeji Oluwatosin suna neman ya bayyana inda ya sa gaba a siyasance.

Kara karanta wannan
An samu akasi harshen Tinubu ya suɓuce, ya tafka kuskure a tsakiyar jama'a a Abuja
Shugabannin na jam'iyyar hamayya sun yi wannan kira ne a wata wasika a fili da suka aika wa Adeleke da shugabannin jam’iyyar na kasa.
Sun bayyana damuwarsu kan yadda shiga kamfen din Tinubu da Adeleke ya yi zai iya rage damar samun nasarar ‘yan takararsu a 2027.
Gwamna ya manta da jam'iyyar Accord bayan zabe?
Adeleke ya lashe zaben gwamnan Osun ne karkashin jam’iyyar Accord amma yanzu yana yi wa APC aiki a zaben shugaban kasa mai zuwa.
Shugabannin sun ce nasarar zaben gwamnan Osun ta kara musu kwarin guiwar cewa jam’iyyar za ta iya zama silar kawo wani sauyin siyasa.
Sai dai sun ce rahoton nadin Adeleke a matsayin jagoran kamfen din Tinubu ya jefa ayar tambaya kan amannar da ya yi da jam'iyyarsa ta Accord.
Suna ganin babu yadda zai iya kare muradun jam’iyyar adawar lokacin da yake aiki da APC.
Suna neman jin yadda wanda ya ci zabe karkashin Accord zai jagoranci kamfen din dan takarar wata jam’iyya, ya rabu da wadanda suka tsaida.
Illar da gwamnan zai yi wa jam'iyyar Accord
'Yan siyasar sun yi gargadin cewa matakin zai iya raunana damar ‘yan takarar jam’iyyar, musamman wadanda za su nemi kujerun majalisa.
Akwai wadanda Accord ta tsaida takarar Majalisar dattawa da Majalisar wakilai a jihar Osun, kuma tana da nata 'dan takaran shugaban kasar.
Sun ce hakan na iya rikitar da masu zabe tare da sace guiwar mambobin da suka kashe kudi da lokacinsu wajen gina jam’iyyar hamayyar.
Shugabannin sun jaddada cewa ba don kiyayya ko hassada suke yin wannan magana ba sai dai kokarin kare muradun jam’iyyar da aka gina.
Haka zalika suna son tabbatar da cewa shugabanninta sun rike alkawuran siyasar da suka yi.
Ana so Gwamna Adeleke ya zabi daya
Sun bukaci Adeleke ya bayyana matsayinsa karara, tare da nuna ko yana ci gaba da biyayya ga Accord wato ko kuwa APC ta rinjaye shi.
Sun kuma bukace shi da ya sake duba rawar da ake cewa zai taka a kamfen din Tinubu idan har yana ci gaba da kasancewa a cikin Accord.
Idan ya sauya matsayinsa na siyasa, ya kamata ya bayyana hakan a fili tare da daukar matakan da dokokin kasa da na jam’iyya suka tanada.
Sun kuma nemi shugabannin Accord na kasa su gaggauta shiga lamarin domin fayyace matsayin Adeleke da kuma kare muradunta.
APC ta sanya wasu ’yan siyasa daga jam’iyyun adawa cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen Bola Tinubu

Source: Twitter
'Yan adawan da ke tallar Bola Tinubu
Rahoto guda ya zo game da yadda APC ta sanya wasu ’yan siyasa daga jam’iyyun adawa cikin kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu.
A ciki har da Nyesom Wike na PDP, Ademola Adeleke da kwanan ya sake cin zabe a jam'iyyar Accord Party da kuma Chukwuma Soludo.
Akwai tsohon mutumin Atiku Abubakar a PDP kuma tsohon kakaki, Segun Sowunmi wanda yanzu yake tallar tazarcen Tinubu sako da lungu.
Asali: Legit.ng

