Kamar Kano, NDC ba Ta da ‘Dan Takarar Gwamna a Kaduna da INEC Ta Fitar da Sunaye
- Jam’iyyar NDC ba ta da wanda zai yi mata takarar gwamnan jiha a Kaduna a zaben da za a yi a badi
- Ba a ga sunan Danjuma Laah ba da hukumar INEC ta saki sunayen karshe na masu neman takara
- Tsohon Sanatan Kaduna ta Kudu, Laah aka yi tunanin zai kalubalanci APC da ADC a zaben Kaduna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kaduna - Jam’iyyar NDC ta tabbata a tsaka mai wuya a jihar Kaduna domin kuwa ba ta da ‘dan takaran gwamna a zaben 2027.
Zuwa yanzu dai babu sunan ‘dan takaran jam’iyyar NDC daga Kaduna cikin jerin masu neman gwamna da INEC ta wallafa.

Source: Facebook
NDC ta gaza magana kan takarar gwamnan Kaduna
Da Leadership ta nemi jin ta bakin Sunday Ibrahim a matsayinsa na shugaban NDC a Kaduna, ya ki yin magana a kan batun.
Evangelist Mordecai Sunday Ibrahim ya ki yi wa ‘yan jarida bayanin abin da ya jawo ba a ga ‘dan takaransa wajen INEC ba.
An yi tunanin cewa Sanata Danjuma Laah zai rike wa jam’iyyar NDC tuta a zaben jihar Kaduna.
INEC ba ta sa sunan 'dan takaran NDC ba
Sai da hukumar zabe ta saki sunaye sai aka nemi tsohon sanatan na Kudancin Kaduna aka rasa, abin da ya zo da mamaki.
Shugaban NDC ya ce ba zai iya yin magana ba da aka kira shi domin ya yi wa ‘yan jam’iyyar, masoya da sauran jama’a bayani.
Rikicin cikin gida ya illata jam'iyyar NDC?
Kafin a kai ga tsayar da Sanata Laah, an ji yadda aka rika kai ruwa-rana a NDC da ta shahara bayan sauya-shekar su Peter Obi.
An samu sabani tsakanin Laah da Barista Mohammed Sani Abbas har kowane bangare yake ikirarin shi yake yin takara a jihar.

Kara karanta wannan
PDP ta shaida matakin da ake dauka game da cire sunayen Pantami da wasu ‘yan takara
Dama can rahoto ya gabata cewa ana tunanin rikicin cikin gida ya ci jam’iyyar NDC, ta gaza samun ‘dan takaran gwamna a Kaduna.
A baya an ji Mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa, Alhaji Sidi Abdul Bomi yana cewa babu wanda NDC ta ba tuta a Kaduna.
Da takarar Laah ta tabbata, hakan yana nufin zai yaki Uba Sani na jam’iyyar APC da Isah Ashiru Kudan da jam’iyyar ADC ta tsaida.
Shi ne zai kasance babban ‘dan takaran da ya fito daga Kudancin jihar Kaduna da rabonsu da gwamna tun Patrick Yakowa.
Haka aka yi a Kano inda yanzu babu sunan Aminu Abdussalam Gwarzo wanda aka yi tunanin shi zai nemi gwamna a 2027.
Tuni dai an fara motsa NDC a jihar Kaduna, Legit Hausa ta lura da takarar Muhammad Turad a matsayin 'dan majalisar dattawa.
Surukin na Muhammadu Buhari yana neman zama sanatan Arewacin jihar Kaduna wanda a yanzu ADC ta ke rike da ita.

Source: Facebook
NDC ta ce babu baraka a jam'iyyar
Labari ya zo cewa a karshe dole jam’iyyar NDC ta tanka rade-radin cewa ana yi wa Peter Obi/Rabiu Kwankwaso zagon-kasa.
Kakakin jam’iyyar, Osi Director ya wanke Sanata Seriake Dickson daga bakin zargin da ake yi masa na yakar 'yan takaransa.
Osi Director ya ce jagoran na NDC bai yi wa jam’iyyar APC mai mulki aiki a boye ta bayan kasa, yana tare da Peter Obi.
Asali: Legit.ng

