'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari kan Sojoji a Yobe

'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari kan Sojoji a Yobe

- 'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari kan wata rundunar sojojin Najeriya a wani yankin jihar Yobe

- 'Yan ta'addan sun kashe sojoji 13 a harin yayin da su ka raunata da dama acikinsu

- Su ma 'yan ta'addan sun rasa wasu rayuwa ka a yayin harin

Sojoji 13 sun mutu a wani kwanton bauna da mayakan kungiyar Islamic State West Africa Province (ISWAP) a yankin arewa maso gabashin Najeriya mai fama da tashin hankali, in ji majiyar wasu sojoji biyu a ranar Litinin.

Wasu manyan bindigogi da rokoki masu linzami sun fada kan ayarin sojoji a kauyen Gazagana, mai nisan kilomita 30 daga Damaturu babban birnin jihar Yobe a ranar Asabar.

Wani jami'in ya ce "Mun rasa sojoji 13 a wannan kwantan baunar kuma da dama sun ji rauni."

KU KARANTA: An kama wasu 'yan fashi 2 biyu a jihar Kano

'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari kan Sojoji a Yobe
'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari kan Sojoji a Yobe Hoto: Vanguard News
Asali: UGC

Ayarin na kan hanyarsu ta zuwa sansanin sojoji da ke Buni Yadi, kilomita 20 daga Damaturu, in ji majiyar sojojin ta biyu, wacce ta bayar da adadin wadanda suka mutu.

"Yaki mai zafi ne kuma 'yan ta'addan suma su samu asara," in ji shi, ba tare da bayar da adadi ba.

Kungiyar ISWAP tana kai hare-hare a kai a kai a yankin Buni Yadi kan sojoji da matafiya, tare da barkewar rikici har cikin jihar Borno.

Tun daga shekara ta 2009, yakin 'yan Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya ya mai da hankali kan Borno inda kungiyar Boko Haram ma ke aiki.

ISWAP ta balle daga kungiyar Boko Haram a shekarar 2016 kuma ta tashi ta zama kungiyar da ke kan gaba.

KU KARANTA: Alurar rigakafin COVID-19 ba ta dauke da microchip, in ji FG ga 'yan Najeriya

Rikicin ya bazu zuwa kasashen Nijar, Chadi da Kamaru da ke makwabtakada arewa maso gabacin Najeriya, lamarin da ya sa kawancen sojoji na yankin yakar mayakan.

Akalla mutane 36,000 ne aka kashe a rikicin, wanda ya raba kimanin miliyan biyu da muhallinsu daga shekarar 2009.

A wani labarin, The Nation ta ruwaito cewa, sojojin Operation TURA TAKAIBANGO sun ce sun kashe wasu 'yan kungiyar Boko Haram a ranar Lahadi a wani gumurzu da suka yi a Gujba, wani kauye da ke karamar hukumar Gujba a jihar Yobe.

A wata sanarwa da mukaddashin Daraktan, Ayyukan Sadarwa na Tsaro, Brig.-Gen. Benard Onyeuko, ya ce sabon aikin Operation TURA TAKAIBANGO ya riga ya samar da sakamako tare da sabon aikin da suka yi.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa an gano tarin makamai da alburusai na ‘yan ta’addan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.