Zulum ya sanya yara sama da 1,000 a makaranta

Zulum ya sanya yara sama da 1,000 a makaranta

- Gwamnan jihar Borno ya sanya yara 'yan gudun hijira 1,163 a makaranta a Damasak

- Gwamnan wanda da kansa ya jagoranci shirin, ya share kwanaki a Damasak don kaddamar da shirin

- Gwamnan ya karfafawa iyaye da masu iyayen rikon yara da su ci gaba da tura yaransu makaranta

Gwamnan jihar Barno Babagana Zulum ya sanya yara 1,163 na mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallinsu a wata makaranta a garin da aka kwato daga hannun masu tayar da kayar baya a jihar, The Sun ta ruwaito.

Gwamnan, wanda ya sanya ido a kan sanya yara 'yan gudun hijirar a garin Damasak, a ranar karshe ta ziyarar da ya kai yankin ranar Litinin, ya ce atisayen wani yunkuri ne na tabbatar da ci gaba mai dorewa.

Ya yi kira ga iyaye da su bar ‘ya’yansu su shiga makarantu.

Ya ce iyaye da masu rikon yara wadanda ke ba wa ‘ya’yansu damar zuwa makarantu ne za a yi la’akari da su game da kunshin walwala da jin dadin jama’a daga gwamnati.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun kame wasu Fulani 47 dauke da makamai a Oyo

Zulum ya sanya yara sama da 1,000 a makaranta
Zulum ya sanya yara sama da 1,000 a makaranta Hoto: The Sun
Source: UGC

Ya ce manufar ita ce a karfafa wa iyaye gwiwa su ilimantar da ’ya’yansu.

Ya tabbatar wa dukkan daliban makarantar sakandare a Damasak da wadanda suka rubuta jarabawar kammala sakandare na goyon bayan gwamnati.

Gwamna Zulum ya kasance a Damasak, mai tazarar kilomita 189 zuwa Maiduguri tun ranar Asabar don raba kayan abinci da sauran taimako ga mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu.

Yawancin 'yan gudun hijirar sun fito ne daga wata karamar hukumar da ke kusa.

Damasak, hedikwatar karamar hukumar Mobbar, ta taba kasancewa matattarar mayakan Boko Haram.

Kungiyar Boko Haram ta lalata kimanin makarantu 1; 400 a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya kuma fiye da rabin makarantun na Borno sun kasance a rufe kusan shekaru goma yanzu saboda tashin hankali, in ji wani rahoto na shekara ta 2017 na UNICEF.

KU KARANTA: Pat Utomi ya siffanta 'yan siyasar arewa da cimma zaune

Kusan dukkan makarantun da ke arewacin Borno, yankin da ke fama da tashe-tashen hankula, kungiyar Boko Haram ta kone yayin da wasu kalilan suka koma sansanonin soja.

A wani labarin daban, Wani dan majalisa, mai wakiltar Bodinga-Dange, a mazabar tarayya ta Shuni-Tureta, Dr. Balarabe Kakale ya ware naira miliyan 200 domin karfafawa Almajiri da kananan ‘yan kasuwa a mazabar sa, Daily Trust ta ruwaito.

A wata hira da aka yi da shi jim kadan bayan rarraba motoci tara, babura 33, kekunan dinki 60, injunan nika 40 da sauransu ga wadanda suka fara cin gajiyar shirin, ya ce an yi hakan ne domin a hana Almajirai yin bara.

Ya kara da cewa yana harin tallafawa almajirai 1000 ne a wannan shekarar kadai, ya kara da cewa shirin zai ci gaba ne.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel