Sojoji Sun Kashe Sama Da 'Yan Bindiga 50, Sun Kwato Dabbobin Da Aka Sace A Zamfara

Sojoji Sun Kashe Sama Da 'Yan Bindiga 50, Sun Kwato Dabbobin Da Aka Sace A Zamfara

- Sojojin Najeriya sun kashe 'yan bindiga a wani yankin jihar Zamfara

- Sojojin sun kwato dabbobi sama da 330 a hannun barayin a yayin arangamar

- Kwamandan sojojin ya karfafawa jaruman sojijin gwiwa tare da yaba aikinsu

A ranar Asabar ne rundunar Operation Hadarin Daji, ta fatattaki 'yan ta'adda akalla 50 a kauyen Kuriya da ke karamar hukumar Kaura Namoda a Zamfara, in ji hedkwatar tsaro.

Mai Gudanarwa a Ayyukan Watsa Labarai na Tsaro, Maj.-Gen. John Enenche ya fada cikin wata sanarwa a ranar Lahadi cewa sojojin sun kuma kwato dabbobi 334 da barayin suka sace a yayin arangamar, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Amurka: Sabuwar Korona ta sake kunno kai a jihohi takwas

Sojoji Sun Kashe Sama Da 'Yan Bindiga 50, Sun Kwato Dabbobin Da Aka Sace A Zamfara
Sojoji Sun Kashe Sama Da 'Yan Bindiga 50, Sun Kwato Dabbobin Da Aka Sace A Zamfara Hoto: Ripples Nigeria
Asali: Facebook

Enenche ya ce sojojin sun yi nasarar ne tare da taimakon saojin sama.

Wannan aiki ya biyo bayan bayanan sirri ne na ayyukan 'yan fashin a wurin.

Ya ce sojoji hudu sun ji rauni a yayin arangamar.

A cewarsa, bayanan sirri na mutane sun tabbatar da cewa an kashe akalla 'yan bindiga 50 a artabun.

“Haka kuma, sojoji sun kwato dabbobi 272 daga hannun‘ yan fashin.

“A wani labarin kuma, sojojin da aka tura kauyen Dunya na karamar hukumar Danmusa ta Katsina sun kuma kwato dabbobi 62 daga hannun 'yan fashin da suka gudu zuwa daji yayin da suka ga sojoji suna sintiri.

KU KARANTA: Jam'iyyar APC na harin samun sababbin mambobi miliyan 2 a Adamawa

“A halin yanzu, jaruman sojojin sun ci gaba da mamaye wuraren tare da yin sintiri don hana masu laifi 'yancin aiwatarwa"

"Babban kwamandan sojan ya yaba wa dakaru tare da karfafa musu gwiwa da kada su huta kan abin da suke kai har sai an dawo da zaman lafiya ga dukkan yankunan kasar da ke fama da rikici," in ji shi.

A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda a Zamfara ta kame mutane 18 da ake zargi a kan wani rikici, wanda ya kai ga lalata dukiya ciki har da fadar Sarkin Shinkafi.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Muhammad Shehu ya fitar a ranar Lahadi a Gusau.

“Matasa dauke da bindigogin dane, adduna da sanduna sun lalata fadar Sarkin Shinkafi da wasu gidaje biyu a garin Shinkafi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel