Bidiyon Yadda Ruwan Sama Ya Ruguza Allon Tallata Tinubu
- Iska mai ƙarfi da ruwan sama sun kifar da allon tallan Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima, a jihar Ogun
- Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a kafar sada zumunta inda wasu suka fassara shi a matsayin alamar sauyin siyasa a zaben 2027
- Mai fafutuka kuma takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, na cikin waɗanda suka yi martani kan lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Wata guguwa mai ƙarfi ta kifar da allon kamfen ɗin Bola/Shettima, a jihar Ogun, lamarin da ya jawo martani daga ’yan Najeriya a kafafen sada zumunta.
Allon, wanda ke ɗauke da hotunan shugabannin biyu, ya zama abin tattaunawa a kafar sada zumunta yayin da wasu suka danganta kifewar da siyasar Najeriya.

Source: Facebook
Leadership ta wallafa cewa wasu masu amfani da kafar sun fassara lamarin a matsayin alamar adawa da jam’iyyar APC, yayin da wasu suka mayar da hankali kan ingancin ayyukan more rayuwa da kuma yadda ’yan adawa ke shirin tunkarar zaɓen 2027.
Yele Sowore: An gaji da Bola Tinubu
Mai fafutuka kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC a, Omoyele Sowore, ya yi martani kan kifewar allon kamfen ɗin.
A wani saƙo da ya wallafa a X, Sowore ya rubuta cewa:
“Yanayi ma ya ƙi jinin Tinubu!
“Har yanayi ma ya gaji da Tinubu. Wata guguwar ruwan sama mai ƙarfi ta kifar da allon kamfen ɗinsa.
“Ga waɗanda suka yi imani da alamomi, hoton yana ɗauke da saƙo mai girma; iskar sauyi ta yi magana. Yanayi ya aika da nasa saƙon!”
Martanin 'yan Najeriya
Bayan kifewar allon, wasu masu amfani da X sun bayyana ra’ayoyinsu kan yadda ’yan adawa za su iya amfani da lamarin wajen yaƙin neman zaɓe.
Wani mai amfani da kafar mai suna @Unkleayo ya ce ya kamata jam’iyyun adawa su yi amfani da bidiyon wajen yaɗa saƙonninsu a harsuna daban-daban.
Ya rubuta cewa bidiyon zai iya zama kayan kamfen na tsawon watan, yana mai cewa ba kowane abu ne ya kamata a riƙa koyar da ’yan siyasa yadda za su yi amfani da shi ba.
Shi kuwa @sabi_engineer7 ya soki APC, inda ya bayyana cewa jam’iyyar ba ta iya yin komai yadda ya kamata, har da gina allon tallan kamfen.

Source: Original
Wani mai amfani da X, @victorrichman, ya danganta lamarin da zargin cin hanci da rashawa, yana mai cewa duk da albarkatun da ake da su, an kasa gudanar da aikin yadda ya kamata.
A nasa ɓangaren, @josiahidam ya fassara kifewar allon a matsayin alamar raunin wa’adin siyasar shugaban ƙasa, yana mai cewa waɗanda suka dogara da wannan wa’adi za su iya fuskantar irin wannan koma baya.
Legit ta tattauna da Sani
Wani dan Arewa da ke aiki a kusa da wajen da abin ya faru a Ogun, Muhammad Sani ya bayyana wa Legit cewa ya ga mutane suna dauke karafunan allon.
Sani ya ce:
"Lallai an yi ruwa mai karfi sosai. Na fita ta kusa da wajen bayan ruwan ya dauke.
"Na ga wasu mutane suna tattara karafunan allon. Babu alamun cewa jami'an tsaro ne, domin sun fi kama da 'yan bangar siyasa."
Ga bidiyon yadda allon ya fado a kasa:
Atiku Abubakar ya bukaci a karbi PVC
A wani labarin, mun ruwaito cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya soki tsadar rayuwa da matsalar tsaro a Najeriya.
Atiku ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya fitar a ranar Laraba, inda ya buƙaci masu rajistar zaɓe su karɓi katunan zaɓensu na dindindin (PVC) gabanin zaɓe mai zuwa.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce ’yan Najeriya na fama da matsin tattalin arziki da rashin tsaro, inda ya bayyana damuwar iyaye kan ciyar da ’ya’yansu.
Asali: Legit.ng


