Dan wasan kwallon Kano Pillars ya bata

Dan wasan kwallon Kano Pillars ya bata

- Wani dan wasan kwallon kafa na Kano Pillars ya bata tsawon makwanni biyu

- Dan wasan da ya tafi hutun kwanaki hudu ba a sake jin duriyarsa ba har yau

- Kulob din kwallon kafa ta bayyana batan sa ne bayan bashi hutu da tayi na kwanaki hudu

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars FC ta bayyana cewa daya daga cikin yan wasanta, Sunday Chinedu ya bata, Daily Nigerian ta ruwaito.

Idris Malikawa, jami'in yada labarai na kungiyar ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Litinin a Kano.

KU KARANTA: APC tayi tir da tarzomar Amurka, ta roki Trump da yayi koyi da Buhari

Dan wasan kwallon Kano Pillars ya bata
Dan wasan kwallon Kano Pillars ya bata Hoto: Kano Pillars
Source: UGC

Malikawa ya ce mai ba da shawara kan fasaha Lionel Soccio ne ya bai wa dan wasan hutun kwana hudu, don ya ziyarci iyalansa, amma har yanzu bai dawo ba makonni biyu kenan.

Ya ce dan wasan bai kuma sanar da kulob din inda yake ba.

“Shugaban kungiyar, Shuaibu Surajo, ya bai wa dan wasan kwanaki uku ya dawo ko kuma ya fuskanci horo.

"Muna yin iya kokarinmu don kare sha'awa da jin dadin 'yan wasanmu, amma kulob din ba zai lamunci rashin da'a daga gare su ba," in ji Malikawa.

KU KARANTA: Amotekun sun kashe uba da 'ya'yansa biyu a Oyo

Ya bukaci dukkan ‘yan wasan kungiyar su ci gaba da mai da hankali kan aikin da ke gabansu.

A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kano ta tabbatar da kame wasu mutane biyu da ake zargi da fashi da makami.

An kuma kwato wata mota da 'yan fashi da makamin suka kwace, yayin da suka kashe mai motar a jihar Kano, Daily Nigerian ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 10 na dare, a kan titin gidan zoo, kusa da Shoprite lokacin da wadanda ake zargin ’yan fashi ne suka harbe direban motar mai suna Isa Hassan Abubakar da ke rukunin gidajen Rijiyar Zaki bayan sun fitar da shi da karfi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel