Jerin Sunayen Mutane 155 da Za Su Taya Gwamna Abba Yakin Neman Zaben Kano
- APC ta fitar da kwamitin da zai yi mata aikin yakin neman zaben shugaban kasa da gwamna a Kano
- Shugaban jam’iyya, Umar Haruna Doguwa ya fitar da sunayen ‘yan kwamitin yakin neman zaben 2027
- Duk wani da ake ji da shi a jam’iyyar APC daga Kano, sai da ya shiga cikin ‘yan kwamitin na kamfe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Jam’iyyar APC ta reshen jihar Kano ta fitar da kwamitin da zai yi mata yakin neman babban zaben da za a yi a 2027.
Za a ga sunaye 130 amma 'yan kwamitin sun kai 155 saboda za a hada da 'yan majalisar Kano da masu-ci da masu takara.

Source: Facebook
An fitar da kwamitin yakin zaben APC a Kano
A Facebook, hadimin gwamna, Ibrahim Adam ya fitar da sanarwar da ta bayyana jerin manyan ‘yan siyasan da aka ba nauyin.
Ibrahim Adam ya bayyana cewa Alhaji Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo zai kula da harkokin kamfe da za a yi a jihar Kano.
An ba shi wannan aiki ne ganin tsohon karamin ministan gidajen shi ne shugaban rikon kwarya na farko na jam’iyyar a jihar.
Nan gaba za a fitar da sunayen wadanda za su yi aiki a sauraron bangarorin kamfe kamar hulda da jama’a, kudi da gudanarwa.
Kamar yadda APC ta saba, gwamna ne shugaban kwamitin, sai mataimakinsa wato Murtala Garo a matsayin mataimaki na I.
Mataimaki na II shi ne shugaban jam’iyya na Kano kuma tsohon kwamishinan ilmi na jihar Kano.
Mutanen da za su yi wa APC kamfe
A kwamitin akwai tun daga Dr. Abdullahi Ganduje, Barau Jibrin da Kawu Sumaila, Kabir Gaya zuwa Malam Ibrahim Shekarau.
Akwai Mariya Mahmoud Bunkure, Bashir Lado, Hafiz Abuabakar da Ahmad Garba Bichi da ministocin Muhammadu Buhari.
Jerin yana kunshe da tsofaffin gwamnonin Kano, sanatoci masu-ci da wadanda aka yi a baya da suke ckin jam’iyyar APC mai mulki.
Haka zalika akwai ministocin Bola Tinubu da tsofaffin ministoci da aka yi daga Kano a mulkin APC.
Cikin kwamitin na kamfe akwai shugabannin majalisar dokoki na da da yanzu da kuma masu rike da APC a mataki na kasa.
Akwai tsofaffin shugabannin jam’iyyar APC da suka shiga majalisun NWC da SWC a baya.
Hadimai da mutanen Tinubu daga Kano sun shiga
Mutanen da shugaban kasa ya ba mukamai irinsu Abdul’aziz Abdul’aziz, Ismaila Ahmed da Ummusalim Isiyaka Rabiu suna ciki.
An ga fitattun ‘yan siyasa kamar Abdulkarim Abdussalam (A.A. Zaura), Rt. Hon. Kabiru Alasan Rurum da Hon. Mustapha Buhari Bakwana.
Hon. Lamin Sani Kawaji, Hon. Ibrahim Ahmed Karaye, Hon. Baffa Muhammad Takai da duk wadanda suka rike ALGON suna nan.
A mata kuwa akwai Baraka Sani, Laila Salisu Buhari, Hajiya Fatima Abdullahi Dala, Bilkisu Maimota da Hajiya Halima Uba Jalli.
Cikakken jerin 'yan kwamitin kamfen APC a Kano
- H.E. Abba Kabir Yusuf
- H.E. Murtala Sule Garo
- Hon. Umar Haruna Doguwa
- Rt. Hon. Jibrin Ismail Falgore
- H.E Dr. Abdullahi Umar Ganduje
- Sen. Barau Ibrahim Jibrin
- Sen. Dr. Suleiman Abdurrahaman Kawu Sumaila
- Sen. Rufai Sani Hanga
- Sen. Arc. Kabiru Ibrahim Gaya
- Sen. Malam Ibrahim Shekarau
- Col. Habibu Shuaibu Rtd.
- Gen. Lawal Jafaru Isa Rtd.
- Col. Yakubu Bako Rtd.
- All Members/Candidates House of Reps. (25)
- Rt. Hon. Yusuf Abdullahi Ata
- Dr. Mariya Mahmoud Bunkure
- Sen. Bashir Lado Garba
- H.E Prof. Hafiz Abubakar
- H.E Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo
- Hon. Ahmad Garba Bichi
- Alh. Muhammad Sabo Nanono
- Gen. Bashir Salihi Magashi
- Gen. Abdulrahman Bello Danbazau
- Hon. Salisu Maje Ahmad Gwangwazo
- Prof. Yusuf Sabo Muhammad
- Hon. Muhammad Jamu Yusuf, MON
- Hon. Abdulhamid Umar (Oscar)
- Hon. Mustapha Hamza Buhari Bakwana
- Sen. Bello Hayatu Gwarzo
- Sen. Mus'ud Eljibrin Doguwa
- Sen. Aminu Sule Garo
- Hon. Bala Muhammad Gwagwarwa
- Hon. Adamu Abdu Panda
- Hon. Ali Ahmed Yako
- Hon. Nasiru Aliko Koki
- Barr. Ismail Ahmad (PCGNi)
- Hon. Baffa Babba Dan Aagundi
- Dr. Aisha Garba
- Engr. Abba Abubakar Aliyu
- Hon. Abdul'aziz Abdul'aziz
- Hajia Ummusalam Isiyaka Rabiu
- Hon. Abdullahi Abbas
- Hon. Abdullahi Zubairu Imam (Abiya)
- Hon. Muhammad Bello Butubutu
- Hon. Lawal Hussain Dala
- Hon. Mudassiru Ibrahim Zawaciki
- Hon. Zubairu Hamza Massu
- Hon. Labaran Abdu Madari
- Hon. Garba Fammar Kibiya
- Hon. Zakariyya Abdullahi Nuhu
- Hon. Abdulkarim Abdussalam (AA Zaura)
- Rt Hon. Kabiru Alasan Rurum
- Rt. Hon. Hamisu Ibrahim Chidari
- Rt. Hon. Yau Abdullahi Yanshana
- Rt. Hon. Alasan Abubakar Kibiya
- Rt. Hon. Gambo Sallau
- Rt. Hon. Balarabe Sa'idu Gani
- Rt. Hon. Abdul'aziz Garba Gafasa
- Rt. Hon. Isiyaku Ali Danja
- Rt. Hon. (Barr) Farouk Iya Sambo
- Hon. Alhaji Usman Alhaji
- Engr. Rabiu Sulaiman Bichi
- Dr. Abdullahi Baffa Bichi
- Dr. Yunusa Adamu Dangwani
- Gwani Dr. Ali Haruna Makoda
- Hon. Usman Bala mni
- Dr. Sulaiman Wali Sani mni
- Hon. Salihu Sagir Takai
- Alh. Sani Isah ASIA
- Alh. Abubakar Sadiq Dangaske
- Barr. Junaidu Muhammad Zakari
- Alh. Audu Ladiyo
- Barr. Gazzali Ahmad Muwaffaq
- Alh. Mamman Maifata UMZA
- Alh. Dayyabu Ahmad Maiturare
- Wada AA Rano
- Alh. Ibrahim Garo
- Sheik Abdullahi Sale Pakistan
- Sheik (Dr.) Aminu Ibrahim Daurawa
- Sheik Ali Dan Abba
- Sheik, Dr. Nazifi Bichi
- Rt. Hon. Aliko Shu'aibu Mukhtar
- Hajia Saadatu Salisu Soja
- Hon. Lamin Sani Kawaji
- Hon. Ibrahim Ahmed Karaye
- Hon. Baffa Muhammad Takai
- Hon. Muntari Ishaq Yakasai
- Hon Ali Datti Yako
- Hon. Dankaka Hussaini Bebeji
- Hajia Yahanasu Buba
- Hajia Aisha Abdullahi Kaita
- Dr. Umar Tanko Yakasai
- Hajiya Fatima Abdullahi Dala
- Hajiya Halima Uba Jalli
- Lami Isa Dawaki
- Hajiya Baraka S Sani
- Hon. Azumi Namadi Bebeji
- Hajia Laila Salisu Buhari
- Hon. Abdullahi Tanko Yakasai
- Prof. Shehu Abdullahi Ma'aji
- Hajia Bilkisu Shehu Maimota
- Gen. A.M Jibrin Tofawa
- Hon. Farouk Lawan
- Comrd Baffa Sani Gaya
- Shiekh Ahmad Tijjani Auwalu
- Dr. Dajuma Mahmoud
- Hon. Hamza Maifata Bichi
- Hon. Jamilu Abubakar Danbatta
- Hon. Imam Yusuf Ogan Boye
- Hon. Dr Abdulhadi Zubairu Chula
- Hon. Zubairu Imam Dala
- Habibu Hassan El-Yakub
- Hon. Rabiu Bako
- Hon. Ibrahim Zakari Sarina
- Air Commodor Yusha'u Salisu T/Wada Rtd
- Barr. Abdulkarim Kabiru Maude, SAN
- Barr. Haruna Isa Dederi
- Barr. Balarabe Bello Rogo
- Hon. Surajo Hamisu Danbatta
- Hon. Wada Doho
- Alh. Yahaya Idris Madobi
- Ado Aminu Kademi
- Alh. Faruk Rabiu Mudi
- Alh. Rabiu Sarkin Fulani Gwarzo
- Hon. Musa Suleiman Shanono
- Hon. Tajuddeen Othman Zaura
- Barr. Muhuyi Magaji Rimin Gado
- Hon. Ismail Gurjiya
- Hon. Wakili Aliyu
- Alh. Umar Farouk Ibrahim
NDC ta ga ta kanta a Kaduna
Rahoto ya zo cewa an kuma samun jihar Arewacin Najeriya da NDC ba ta da ‘dan takaran gwamna a zaben shekarar 2027.
Wannan ya yi kama da abin da ya faru da magoya bayan Kwankwasiyya a jihar Kano dababu sunan Aminu Abussalam Gwarzo.
Shugaban jam'iyyar NDC na reshen Kaduna ya yi gum da aka bukaci jin halin da ake ciki a yanzu.
Asali: Legit.ng


