Wani dan majalisa zai tallafawa Almajirai da kudi N200m

Wani dan majalisa zai tallafawa Almajirai da kudi N200m

- Wani dan majalisa a jihar Sakkwato ya shirya yi wa Almajirai goma ta arziki

- Dan majalisan tuni ya fara rabawa Almajiran da marasa karfi babura, injunan nika da sauransu

- Dan majalisar ya bayyana wannan shiri ne zai ci gaba da gudana a karkashinsa

Wani dan majalisa, mai wakiltar Bodinga-Dange, a mazabar tarayya ta Shuni-Tureta, Dr. Balarabe Kakale ya ware naira miliyan 200 domin karfafawa Almajiri da kananan ‘yan kasuwa a mazabar sa, Daily Trust ta ruwaito.

A wata hira da aka yi da shi jim kadan bayan rarraba motoci tara, babura 33, kekunan dinki 60, injunan nika 40 da sauransu ga wadanda suka fara cin gajiyar shirin, ya ce an yi hakan ne domin a hana Almajirai yin bara.

Ya kara da cewa yana harin tallafawa almajirai 1000 ne a wannan shekarar kadai, ya kara da cewa shirin zai ci gaba ne.

A cewarsa, an kuma samar da kudin ne don karfafa Makarantun Allo (makarantun Alkur'ani) da Malaman su.

KU KARANTA: 'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari kan Sojoji a Yobe

Wani dan majalisa zai tallafawa Almajirai da kudi N200m
Wani dan majalisa zai tallafawa Almajirai da kudi N200m Hoto: BBC Hausa
Source: UGC

“Wannan shine dalilin da ya sa muka rarraba kananan motoci guda 4 zuwa Makarantun Allo da babura 33 ga Malamansu, wadanda za su iya amfani da su wajen samar da kudin shiga.

"Kuma mun bai wa masu karatun Makarantun Allo, mata da mutane masu fama da nakasa da sauran 'yan kasuwa karfin gwiwa da kayayyakin aiki da kuma rancen da ba ruwa," in ji shi.

Ya bayyana cewa an yiwa aikin lakabin "Kowa Ya Iya Allon shi, sai shi wanke," saboda an yi shi ne don sanya Almajirai su dogara da kansu.

Kakale wanda ake kira da suna "Memba mai Allo" don yin gwagwarmayar tabbatar da Almajiri a kasar, ya kara da cewa an kafa kwamiti da zai bibiyi ayyukansu tare da tabbatar da cikakken dawo da bashin.

"Saboda abokan huldarmu na banki sun yi alkawarin bayar da kudin da ya dace, idan aka samu nasarar kwato kudaden," in ji shi.

Kakale wanda ya kasance mai daukar nauyin dokar sauya fasalin almajiranci a karamar majalisar, ya nuna adawa ga tsarin almajiranci saboda tsarin karatunsu ba ya karfafa kwazo.

Ya kuma lura cewa gwamnatin tarayya na shirin fitar da ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga kangin talauci, ba zai yi nasara ba, ba tare da damawa Almajirai ba.

Ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari, Ministocin Harkokin Jin Kai, Harkokin Mata da gwamnatin jihar Sakkwato kan yadda suka nuna damuwa kan halin da Almajirai ke ciki a kasar.

KU KARANTA: Dan wasan kwallon Kano Pillars ya bata

A wajen bikin rabon kayayyakin da aka gudanar a karamar hukumar Bodinga da ke jihar Sakkwato, Ministar Harkokin Jin Kai, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta ce gwamnatin tarayya za ta goyi bayan duk wani yunkuri na sauya tsarin karatun almajirai a kasar.

Dakta Umar Bindir wanda ya wakilce ta ya ce “za mu yi amfani da wannan shirin a matsayin samfuri don magance matsalar almajiranci a kasar."

Hadaddiyar kungiyar da ke daukar nauyin karatun Almajiri, Hajiya Aishat Jibril Dukku ta yaba wa takwararta kan wannan aikin karramawa.

A wani labarin daban, Kimanin matan karkara dubu dari da ashirin da biyar a fadin jihohi 36 na tarayyar da kuma Babban Birnin Tarayya (FCT) za su karbi N20,000 kowannensu a matsayin tallafin kudi daga Gwamnatin Tarayya, This Day ta ruwaito.

Ministar jin kai da walwalar jama'a, Sadiya Umar Farouq ne ta bayyana hakan jiya a Kano yayin kaddamar da shirin a jihar.

Game da tallafin kudin a Kano, ta ce kimanin mata 8,000 a duk fadin kananan hukumomin 44 za su ci gajiyar shirin Gwamnatin Tarayya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel