Magana Ta Fito daga Bakin Minista, An Ji Adadin Shekarun da Tinubu ke Bukata a kan Mulki

Magana Ta Fito daga Bakin Minista, An Ji Adadin Shekarun da Tinubu ke Bukata a kan Mulki

  • Ministan Ayyuka, David Umahi, ya buƙaci ’yan Najeriya su sake ba Shugaba Bola Tinubu wa’adin shekaru huɗu domin kammala ayyukan titunan da ya fara
  • Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da aikin gyarawa da faɗaɗa babbar hanyar Lambata zuwa Kontagora mai tsawon kilomita 401
  • Gwamnan Neja, Mohammed Umaru Bago, ya yi alƙawarin cewa jihar za ta samar wa Tinubu mafi yawan ƙuri’u a ƙasar a zaɓe mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Niger, Nigeria - Ministan Ayyuka, David Umahi, ya buƙaci ’yan Najeriya su sake ba Shugaba Bola Tinubu wa’adin shekaru huɗu domin ya kammala ayyukan gine-ginen titunan da gwamnatinsa ta fara a faɗin ƙasar.

Umahi ya yi wannan kira ne a ranar Talata a Ƙaramar Hukumar Bida ta Jihar Neja, yayin bikin aza harsashin aikin sake gina da kuma faɗaɗa babbar titin Lambata–Kontagora mai tsawon kilomita 401.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi sabon bidiyo ya kira Tinubu da 'Bola' duk da APC ta yi gargadi

Umahi.
Ministan ayyuka na Najeriya, David Umahi a ofishinsa da ke ma'aikatar ayyuka a Abuja Hoto: Ifeanyi Chikwuma Odii
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa aikin wannan titi zai lakume kudi wadda kuɗi har Naira tiriliyan 1.5.

Ya bayyana aikin a matsayin wani ɓangare na shirin gwamnatin Tinubu na bunƙasa ababen more rayuwa.

Abin da Tinubu ke bukata daga yan Najeriya

Umahi ya yi ikirarin cewa shugaban ƙasar na buƙatar ƙarin wa’adin shekaru huɗu daga yan Najeriya domin kammala dimbin ayyukan titunan da aka fara a faɗin Najeriya.

Umahi ya ce aikin babbar hanyar Neja shi ne aiki na biyar cikin manyan ayyukan titunan da gwamnatin Tinubu ta ɗauka a matsayin gadonta.

Ya danganta muhimmancin aikin da girmansa, amfani da siminti mai ƙarfe wajen gina shimfiɗar titi da kuma haɗin gwiwar Ƙungiyar Kamfanonin Dangote ƙarƙashin tsarin gwamnatin tarayya na biyan haraji.

“Shugaba Bola Tinubu na buƙatar ƙarin wa’adin shekaru huɗu domin kammala dimbin ayyukan gine-ginen titunan da ya fara a wannan wa’adin mulkinsa a faɗin ƙasar. Gwamnatinsa ta himmatu wajen inganta ababen more rayuwa na tituna a dukkan yankunan siyasa da ƙasa ta kasu.

Kara karanta wannan

Shettima ya magantu a kan tsoron da 'yan Arewa ke ji a tazarcen Tinubu

“Shirin bunƙasa ababen more rayuwa da Shugaba Bola Tinubu ke aiwatarwa ya shafi jihohi da dama, inda Jihar Neja ke cin gajiyar kaso mai tsoka na ayyukan gine-ginen tituna.
“An kammala tituna masu tsawon kilomita 162 da gadoji masu tsawon mita 115 a yankin Arewa ta Tsakiya.”

- David Umahi.

Ministan ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, bisa jarin da ya zuba wajen bunƙasa ababen more rayuwa,

Bago ya yi alƙawarin ƙuri'u ga Tinubu

Gwamna Mohammed Umaru Bago, wanda ya wakilci shugaban ƙasa a wajen bikin ƙaddamar da aikin, ya bayyana babban titin a matsayin wani gagarumin aiki da zai inganta sufuri tsakanin sassa daban-daban na ƙasar.

Gwamna Mohammed Umaru Bago.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago yana jawabi a wurin taro Hoto: Umaru Mohammed Bago
Source: Facebook

Gwamnan ya yi alƙawarin cewa Jihar Neja za ta samar wa Tinubu mafi yawan ƙuri'u a duk faɗin Najeriya a zaɓe mai zuwa, yana mai danganta hakan da jarin da gwamnatin tarayya ta zuba wajen ayyukan more rayuwa.

APC ta hango nasarar Tinubu

Kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki ta sake jaddada cewa Shugaba Bola Tinubu ne zai samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Shugaban Jam’iyyar, Nentawe Yilwatda, ya ce binciken cikin gida da alƙaluman da suka tara sun nuna cewa Tinubu yana gaba da kowane dan takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262