2027: Dattijon Arewa da Ya Yi Siyasa da Sardauna Ya Yi Maganganu kan Tinubu
- Alhaji Tanko Yakasai, mai shekara 100, ya yi wa Shugaba Bola Tinubu fatan samun nasara a zaben shugaban kasa na 2027
- Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya ce yana ganin alamun nasarar Tinubu a zaben 2027, tare da alkawarin jagorantar yakin neman zabensa
- Atiku Abubakar kuma ya bukaci ’yan Najeriya su karbi katin zabe na PVC domin su samu damar neman sauyi ta hanyar kada kuri’a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Dattijon Najeriya, Alhaji Tanko Yakasai, ya yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu fatan samun nasara a zaben shugaban kasa da za a gudanar a 2027.
Yakasai, wanda ya ce an haife shi a shekarar 1925, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin kaddamar da majalisar yakin neman zaben shugaban kasa ta jam’iyyar APC a Abuja.

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa ya gode wa Tinubu da shugabannin APC bisa gayyatar da suka yi masa, yana mai cewa taron ya ba shi damar sake haduwa da tsofaffin abokansa da abokan siyasa.
Maganar Yakasai kan Tinubu
Da yake jawabi a wajen taron, Tanko Yakasai ya bayyana farin cikinsa na ganin Allah Ya tsawaita rayuwarsa har zuwa wannan lokaci.
Ya ce:
“Ina kuma son mika sakon fatan alheri ga shugaban kasa, Shugaba Ahmed Bola Tinubu, tare da yi masa fatan nasara a zabe mai zuwa.”
Dattijon ya kuma gode wa shugaban kasar bisa ba shi damar yin magana a wajen taron, tare da yabawa shugabannin APC saboda karrama shi da gayyatar da suka yi masa.

Source: Facebook
Yakasai ya bayyana cewa, saboda an haife shi a shekarar 1925, ba ya tsammanin akwai wani mahalarci a wajen taron da zai iya kiransa da tsaransa.
Ya kammala jawabinsa ne da yi wa mahalarta taron fatan alheri da addu’ar Allah Ya sanya albarka a cikin al’amuransu.
Hasashen Adeleke kan 2027
A nasa jawabin a wajen kaddamar da majalisar yakin neman zaben APC, Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya ce yana iya hango nasarar Tinubu a zaben 2027.
Punch ta wallafa cewa Adeleke ya bayyana cewa a shirye yake ya jagoranci tafiyar yakin neman zaben shugaban kasar.
Ya ce babu wanda zai iya dakatar da wannan tafiya, yana mai alkawarin cewa magoya bayan Tinubu za su yi murnar komawarsa fadar shugaban kasa ta Aso Rock.
Gwamnan, wanda aka san shi da rawa a tarukan jama’a, ya ce yakin neman zaben zai kasance tare da waka da rawa.
Atiku ya yi magana kan 2027
A wani labarin, kun ji cewa Atiku Abubakar ya bukaci ’yan Najeriya su yi amfani da damar kada kuri’a domin neman sauyin shugabanci ta hanyar lumana.
Ya bayyana cewa matsin tattalin arziki, tsadar rayuwa da rashin tsaro na jefa iyalai cikin damuwa, lamarin da ya ce ya kamata masu kada kuri’a su yi la’akari da shi yayin zaben shugabanni.
Atiku ya kuma bukaci masu rajistar zabe su karbi katin PVC dinsu, yana mai cewa katin zai ba su damar zabar wanda suke ganin zai kawo sauyin da suke bukata.
Asali: Legit.ng

