Bayan Rage Farashi, Gwamnatin Tinubu Ta Yi Bayani kan Yiwuwar Dawo da Tallafi Fetur kafin 2027

Bayan Rage Farashi, Gwamnatin Tinubu Ta Yi Bayani kan Yiwuwar Dawo da Tallafi Fetur kafin 2027

  • Gwamnatin tarayya ta ce ba za ta dawo da tallafin man fetur ba, tana mai cewa zai iya lakume sama da Naira tiriliyan 20 a shekara
  • Ministan Kuɗi, Taiwo Oyedele, ya ce dawo da tallafin na iya lalata darajar Naira zuwa kusan N3,000 kan Dala guda cikin watanni
  • Ya ce cire tallafin mai ya samar da Nair tiriliyan 15.8 ga Asusun Tarayya tsakanin watan Yuni 2023 zuwa Disamba 2025

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ta yi watsi da yiwuwar dawo da tallafin man fetur a Najeriya.

Gwamnatin ta yi ikirarin cewa dawo da tallafin zai iya lakume sama da Naira 20 a kowace shekara tare da lalata darajar Naira zuwa kusan N3,000 kan kowace dala guda.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Mutane 5 'yan gida 1 sun mutu daga kamuwa da cuta a Kano

Oyedele.
Ministan kudi da harkokin tattalin arziki na Najeriya, Taiwo Oyedele a ofis a Abuja Hoto: Taiwo Oyedele
Source: Twitter

Leadership ta ruwaito cewa Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Tattalin Arziki, Farfesa Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a wani taron manema labarai a Abuja.

Oyedele ya fadi haka ne yayin fa yake mayar da martani ga shawarwarin dawo da tallafin, ciki har da wani tsari da aka bayyana a matsayin “tallafin samar da mai” ga matatun mai na cikin gida.

Ministan ya ce ba zai yi jayayya da manufar waɗanda suka gabatar da shawarwarin dawo da tallafin ba, amma gwamnati ba ta yarda da matakin da suke ganin ya kamata a ɗauka ba.

“Tallafi ba ya rage farashin man fetur. Abin da yake yi kawai shi ne sauya yadda ake biyan kuɗin da kuma lokacin biyan sa,” in ji shi.

Gwamnati ta fadi illar dawo da tallafi

Taiwo Oyedele ya ce Najeriya na amfani da kusan lita miliyan 50 na man fetur a kowace rana.

Kara karanta wannan

An zo wajen: An fara shirin daina kai shanu daga Arewa zuwa Kudu

Ya ce mayar da farashin man fetur zuwa matakin da yake kafin cire tallafi zai jawo lashe sama da Naira tiriliyan 20 a shekara, kafin a ƙididdige yiwuwar ƙarin amfani da man da kuma fasa-kwaurin sa.

Ya ce ko farashin N500 kan kowace lita da wasu suka yi alkawarin samarwa zai ci sama da N16trn a shekara.

A cewarsa, wannan kuɗi ya kusan kai wa dukkan kuɗin da Asusun Tarayya ya raba tsakanin matakai uku na gwamnati a shekarar 2025.

Tinubu da gidan mai.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da wani gidan mai a Najeriya Hoto: @DOludegun
Source: Getty Images

Naira na Iya kai wa N3,000

Ya ce ci gaban da aka samu wajen rage hauhawar farashi, wanda ya ba Babban Bankin Najeriya damar fara rage yawan kuɗin ruwa, shi ma na iya shiga cikin haɗari.

“Hasashenmu shi ne cewa farashin musayar kuɗi na iya kusantar N3,000 kan Dala cikin watanni, kuma abin da ake kira man fetur mai tallafi zai kai aƙalla N2,000 kan kowace lita,” in ji shi.

Ministan ya ƙara da cewa wannan farashin ya fi abin da ’yan Najeriya ke biya a yanzu, kamar yadda tashar Channels tv ta rahoto.

Gwamnatin Tinubu ta yi rangwame

Kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za a sayar da fetur mai rahusa a gidajen mai na NNPC na tsawon kwanaki 30.

Ministan kudi, Taiwo Oyedele ya kuma bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta samar da wani sabon tsarin farashin sayo fetur da aka cimma ta hanyar tattaunawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262