IPPIS: SSANU, NASU suna zanga-zangar lumana

IPPIS: SSANU, NASU suna zanga-zangar lumana

- Wasu kungiyoyin malaman jami'a sun fito zanga-zangar lumana a babban birnin tarayya Abuja

- Kungiyoyin sun fito ne dan nuna kokensu dangane da tsarin IPPIS

- Sun kuma bayyana kukansu na rashin biyan wasu daga cikin ma'aikatansu tsawon watanni shida

Bangaren Jami’ar Bayero na Kwamitin Hadin Gwiwa na Manyan Ma’aikatan Kungiyar Jami’o’in Najeriya (SSANU) da kungiyar ma’aikatan jami’o’i marasa ilimi (NASU) sun shiga zanga-zangar lumana, Daily Trust ta ruwaito.

Sun shiga zanga-zangar ne a duk fadin kasar kan rashin kyakkyawan yanayin aiki watanni uku bayan Yarjejeniyar Fahimta da suka yi tare da gwamnatin tarayya.

Zanga-zangar wacce aka shirya za a kwashe kwanaki uku ana gudanar ta, ta jawo cece-kuce sakamakon jinkirin da gwamnatin tarayya ta yi na aiwatar da yarjejeniyar MoU tare da kungiyoyin kwadago a lokacin da suka fara yajin aikin gargadi na mako biyu don matsawa gida bukatarsu a Oktoba a bara.

KU KARANTA: Wani dan majalisa zai tallafawa Almajirai da kudi N200m

IPPIS: SSANU, NASU suna zanga-zangar lumana a BUK
IPPIS: SSANU, NASU suna zanga-zangar lumana a BUK Hoto: The Nation
Source: UGC

Membobin kungiyoyin kwadagon sun hada baki sun bayyana korafinsu game da rashin tsari da ke tattare da sabon tsarin biyan albashi (IPPIS) wanda a karkashinsa aka ce wasu ma’aikatan sun yi asarar sama da 40% na albashinsu ba bisa ka’ida ba.

Wannan zanga-zangar na zuwa ne kusan mako guda da sake bude jami'o'in bayan rufe su watanni tara saboda yajin aikin ASUU kan tsarin biya ta bai daya.

Zanga-zangar ta kasance ta hanyar jerin gwanon lumana daga filin taro na cibiyar zuwa ginin majalisar dattijai inda mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Adamu Sagir Abbas ya yi jawabi ga ma’aikata masu zanga-zangar.

Da suke gabatar da wasikar korafin ga VC don isar da su zuwa ga Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, Shugaban SSANU na Jami'ar, Dakta Haruna Aliyu ya gano rashin daidaito a cikin albashin su na wata saboda IPPIS a matsayin babban abin da ke damun su.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun kame wasu Fulani 47 dauke da makamai a Oyo

IPPIS: SSANU, NASU suna zanga-zangar lumana a BUK

IPPIS: SSANU, NASU suna zanga-zangar lumana a BUK

IPPIS: SSANU, NASU suna zanga-zangar lumana a BUK

IPPIS: SSANU, NASU suna zanga-zangar lumana a BUK

Sun kuma yi kira ga gwamnati da ta hanzarta aiki don magance matsalar kuma wataƙila wasu da ke cikin MoU ɗin da ta sanya hannu.

A wani labarin daban, Malaman jami’a a ranar Litinin sun bayyana shirye-shiryensu na ci gaba da harkokin karatunsu a ranar Litinin mai zuwa kamar yadda Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ta umurce su, The Nation ta ruwaito.

Malaman, sun roki Gwamnatin Tarayya da ta tabbatar musu da lafiyar su da ta daliban su a yayin da ake kokarin shawo kan cutar ta COVID-19.

Shugaban Kungiyar Malaman Jami'o'in (ASUU), Farfesa Biodun Ogunyemi, ya ce tantancewar da rassanta suka yi ya nuna cewa mahukuntan jami'ar ba su yi abin da ya kamata ba don tabbatar da yanayin koyo mai inganci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel