Yanzu yanzu: Kotu ta bayar da belin Sowore a kan kudi Naira miliyan 20

Yanzu yanzu: Kotu ta bayar da belin Sowore a kan kudi Naira miliyan 20

- Kotu ta bada belin dan gwagwarmaya Sowore a kan makudan Naira miliyan 20

- Kotun ta kuma bukaci ya kawo mai tsaya mishi da yakai mataki na 12 a aikin gwamnati

- Sowore zai ci gaba da zuwa duk ranar Litinin da Juma'a kotu don sanya hannu

Wata Babbar Kotun Majistare da ke zaune a Wuse Zone 2, Abuja ta ba da belin mai gabatar da zanga-zangar #RevolutionNow, Omoyele Sowore a kan kudi Naira miliyan 20.

Wanda ake kara na biyu kuma ya bayar da belin su a kan kudi Naira miliyan daya da kuma mutum daya da zai tsaya musu.

Babban alkalin kotun, Mabel Segun-Bello yayin da take yanke hukunci kan neman belin a ranar Litinin ta bayar da belin Sowore a kan kudi Naira miliyan 20 da kuma mutane biyu da za su tsaya masa.

KU KARANTA: Alurar rigakafin COVID-19 ba ta dauke da microchip, in ji FG ga 'yan Najeriya

Yanzu yanzu: Kotu ta bayar da belin Sowore a kan kudi Naira miliyan 20
Yanzu yanzu: Kotu ta bayar da belin Sowore a kan kudi Naira miliyan 20 Hoto: ChannelsTv
Source: UGC

Kotun ta kuma umarci Sowore da ya ci gaba da zama a Abuja kuma dole ne ya gabatar da kansa ga rajistaran kotu a kowace Litinin da Juma'a har sai an saurari hukuncin da aka yanke masa.

Kotun ta kuma ba da umarnin cewa daya daga cikin wadanda za su tsaya masa dole ne ya kasance ma'aikacin gwamnati wanda bai gaza mataki na 12 ba.

Sowore tare da wasu mutane hudu na fuskantar shari'a kan zargin haramcin taro, hada baki, da kuma tayar da hankalin jama'a.

‘Yan sanda sun kame su ne a jajibirin sabuwar shekara yayin wata zanga-zangar adawa da rashin kyakkyawan shugabanci.

KU KARANTA: An kama wasu 'yan fashi 2 biyu a jihar Kano

Sowore a baya kafin zanga-zangar ya tuhumi ‘yan Najeriya a shafin Twitter da su gudanar da zanga-zanga ta hanyar daukar kyandir da tambari da ke nuna korafinsu kan gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Wannan ba shine karo na farko da a ka kama Sowore ba. An tsare shi sama da kwanaki 100 a 2019 saboda kira ga #RevolutionNowProtest.

A wani labarin daban, Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa: Kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Scio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP) ta aika da “korafi cikin gaggawa zuwa ga Kungiyar Hadin Kan Majalisar Dinkin Duniya kan Tsarewa Ba Bisa Ka'ida ba, azabtarwa da sauran muzgunawa da ake wa dan jarida Omoyele Sowore da wasu 'yan gwagwarmaya hudu, saboda kawai sun gudanar da aikinsu na dan Adam cikin lumana.”

SERAP ta ce: "Kamata ya yi Kungiyar ta nemi hukumomin Najeriya su janye tuhumar da ake yi wa Mista Sowore da wasu masu fafutuka hudu, kuma a gaggauta sakinsu ba tare da wani sharadi ba."

A cikin korafin da aka gabatar a ranar 4 ga Janairu, 2021, kuma ya samu sanya hannun mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, kungiyar ta ce: “Tsare Omoyele Sowore da wasu masu fafutuka hudu ya nuna hana su 'yanci ba tare da dalili ba saboda ba ta da wata hujja ta doka."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel