Pat Utomi ya siffanta 'yan siyasar arewa da cimma zaune

Pat Utomi ya siffanta 'yan siyasar arewa da cimma zaune

- Wani farfesa ya siffanta 'yan siyasar arewacin Najeriya da matsorata wajen gyara fasalin kasar

- Ya siffanta su da masu dogaro da kudin shiga da gwamnatin tarayya ke zuba musu

- Ya kiraye su da su hada kai a gyara fasalin kasar domin ci gaban kasar baki daya

Pat Utomi, wani farfesa kan tattalin arzikin siyasa, ya ce wasu ‘yan siyasa a arewa na tsoron sauya fasalin kasa saboda ba su da tabbacin inda zai kai su, The Cable ta ruwaito.

Da yake magana a wata kafar yada labarai ta zamani gabanin taron ‘Never Again’ don tunawa da shekaru 51 bayan yakin basasa, Utomi ya ce arewa ta fi dogara ga gwamnatin tarayya saboda kason da take samu na kudaden shiga, wanda “ya sanya su rashin tabuka komai”.

KU KARANTA: An kama wasu 'yan fashi 2 biyu a jihar Kano

Pat Utomi ya siffanta 'yan siyasar arewa da ciman zaune
Pat Utomi ya siffanta 'yan siyasar arewa da ciman zaune Hoto: The Guardian
Source: UGC

"Akwai rikicin gaske a arewa wanda kudu bata fahimta ba. Wasu mutane ne wadanda suke matukar kiyayya da juna; wannan ita ce gaskiyar magana.

"Shi ya sa suke jin tsoron sake fasalin kasar saboda ba su sani ba inda za ta jagorance su, a wajen Najeriya kuma, ba su da tsari; babu arewa, "

Utomi, duk da haka, ya bukaci 'yan arewa da su yi watsi da irin wannan fargabar, yana mai cewa sake fasalin zai taimaka musu "su zama masu amfani kuma su fice daga matsayin talauci".

Farfesan ya kuma sanar da taron karo na biyu na ‘Never Again’, wanda ya ce zai gayyaci Matthew Kukah, bishop na darikar Katolika ta Sakkwato, a matsayin babban mai gabatar da jawabi.

Ya kuma bayyana cewa a taron na gaba, tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo zai kasance babban bako na musamman.

Ya kara da cewa, Ayo Adebanjo, shugaban Afenifere, da Kalu Idika Kalu, tsohon ministan kudi ne za su jagoranci taron.

KU KARANTA: Amotekun sun kashe uba da 'ya'yansa biyu a Oyo

“A tuna cewa Nijeriya ta yi yakin basasa mai tsawon watanni 30 wanda ya bar ta a cikin rabuwar kai, tashin hankali, da shakkar juna, kiyayya da bacin rai a tsakanin bangarorin da yankin kasar.

"An kiyasta kimanin wadanda aka kashe miliyan daya nan take a lokacin yakin” inji shi

“Taron zai haskaka batutuwan da suka haifar da yakin basasa da kuma bukatar masu kishin kasa su hada kai don cimma daidaito na kasa, musamman ta la’akari da wasu kudurorin da ake da su a cikin siyasa."

A wani labarin daban, Revd. Matthew Kukah, bishop na Katolika na Sakkwato, ya sake caccakar gwamnatin Najeriya.

Kukah a cikin hudubarsa ta baya-bayan nan ya koka kan yadda Najeriya ta zama kazamar kasa, cike da tarkace, yaudara, karya, cin amana, da kuma rikita-rikita inda duhu ya mamaye komai.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 6 ga watan Janairu, yayin da yake gabatar da hudubarsa a babban cocin Katolika na St Joseph, Kaduna, a lokacin da ake gudanar da hidimar Archbishop Peter Yariyock Jatau, Archbishop na Kaduna Catholic Diocese.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel