Gwamnatin tarayyar Najeriya
Masu kiwon kaji sun bukaci gwamnati ta bari a shigo da waken soya da masara don karfafa kiwon kaji a fadin kasa. Sun nuna rashin jin dadinsu ga farashin abinci.
Wani dan Najeriya mazauni kasar Ghana ya gurfana gaban wata kotu da zargin fasa wani dakin ajiya tare da sace tayal da darajarsa ya kai zunzurutun kudi $50,000.
Shugaban Najeriya ya umarci sakin $20m cikin gaggawa ga ECOWAS don magance ta'addanci a yankin Afrika ta yamma. Shugaban ya kuma bukaci sake fasalin ECOWAS.
Gwamnan jihar Neja ya bukaci babbar alkalin jihar da majalisa su fiida hukunci mai tsauri ga masu bai wa 'yan fashi bayanai. Ya bayyana cewa duk laifinsu daya.
'Yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban wata karamar hukuma a jihar Taraba. Daga bisani kuma 'yan bindigan sun bayyana cewa sun kashe shugaban karamar hukumar.
Wasu masu fada aji a jam'iyyar APC sun bayyana suna son barin matasa su ci gaba da jan ragamar jam'iyyar don kawo sauyi a tafiyar siyasar jam'iyyar a nan gaba.
'Yan damfara da sunan masu bincike kan kwayar cutar Korona sun bayyana a babban birnin tarayya Abuja. Hukuma na ci gaba da bincike don kame bata garin a birnin.
Wasu sarakunan gargajiya a jihar Ondo sun bayyana cewa korar Fulani a jihar Ondo ba daidai bane. Sun ce kamar kowa Fulani suna da 'yan zama a ko'ina a kasar.
Hukumar Hisbah a jihar Kano ta bayyana cewa ta sasanta sama da ma'aurata 3,000 a shekarar 2020. Hukumar ta kuma tallafawa al'umma ta fuskoki daban-daban a Kano.
Gwamnatin tarayyar Najeriya
Samu kari