'Yan Najeriya Za Su Yi Farin Ciki da Abin da Yan Sanda Za Su Aikata a Babban Zaben 2027'

'Yan Najeriya Za Su Yi Farin Ciki da Abin da Yan Sanda Za Su Aikata a Babban Zaben 2027'

  • Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Olatunji Disu, ya sha alwashin cewa yan Najeriya za su yi alfahari da rawar da yan sanda za su taka a zaben 2027
  • Ya ce yadda ’yan sanda za su gudanar da ayyukansu kafin zaɓen, lokacin zaɓen da bayan an kammala, zai sa ’yan Najeriya su yi farin ciki da alfahari
  • Disu ya ce rundunar ’yan sanda ta gudanar da taro da kwamishinonin ’yan sanda daga faɗin ƙasar domin karisa shirye-shirye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Sufeto-Janar na ’Yan Sanda (IGP), Olatunji Disu, ya bayyana cewa yadda jami’an ’yan sanda za su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata a babban zaɓen 2027.

Shugaban rundunar yan sandan Najeriya ya ce ayyukan da dakarunsa za su a lokacin zaɓen da kuma bayan an kammala shi, zai sa ’yan Najeriya su yi farin ciki da kuma alfahari da su.

Kara karanta wannan

Ana shirin zaben 2027, shugaban INEC ya mika dukan lamuransa ga Ubangiji

Disu.
Sufeto Janar na rundunar yan sandan Najeriya, Olatunji Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

IGP Disu ya ba yan Najeriya tabbaci

Disu ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa rundunar ’yan sandan ƙasar za ta gudanar da ayyukanta cikin ƙwarewa da bin ƙa’idojin aiki yayin zaɓen da ke tafe, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan ƙaddamar da littafin The Origin of Women in Nigeria Police Force.

Dame Stella Okuyiga, mai shekara 96 kuma tsohuwar mataimakiyar kwamishinan ’yan sanda mai ritaya, ce ta rubuta wannan littafi. Okuyiga na cikin mata 20 na farko da suka shiga rundunar ’yan sandan Najeriya (NPF).

Yan sanda sun fara shirin zaben 2027

Da aka tambaye shi game da zaɓen 2027, IGP ya ce sun shirya taro da kwamishinonin ’yan sanda daga faɗin ƙasar domin tabbatar da cewa jami’an sun gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa a lokacin zaɓen.

“Ina so in sanar da ku cewa mun kammala taron kwamishinonin ’yan sanda da sauran manyan jami’ai. Kwanan nan mun gudanar da zaɓuka biyu ko uku, kuma za ku iya ganin cewa ’yan sanda sun yi aiki mai kyau, mu ma mun yi namu,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi sabon bidiyo ya kira Tinubu da 'Bola' duk da APC ta yi gargadi

Yan sanda.
Dakarun rundunar yan sandan Najeriya a wurin aikin zabe a jihar Osun Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Ya ƙara da cewa sun tattara darussan da suka koya daga zaɓukan da suka gabata, ciki har da wuraren da suka yi nasara da kuma inda suka samu matsala, domin inganta ayyukansu a babban zaɓen da kowa ke sa ido a kansa.

“Na ba ku tabbaci. Rundunar ’yan sandan Najeriya za ta yi aiki mai kyau sosai, za mu sa rundunar ta yi alfahari da kanta, kuma za mu sa ’yan Najeriya su yi alfahari da ita,” in ji Disu.

Dalilin yan sanda na kama Okorocha

Kun ji cewa Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta tabbatar da kama tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha tare da bincikarss kafin ta sallame shi a Abuja

Rundunar ta ce kama Okorochia na da alaƙa da zargin haɗa baki wajen aikata laifi, ƙirƙirar takardun bogi da sojan gona a wata takardar korafi kan zaben fitar da gwanin APC na sanata a Imo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262