‘Yan Bindiga sun sace marayu 8 da wasu 3 a gidan marayu na Abuja

‘Yan Bindiga sun sace marayu 8 da wasu 3 a gidan marayu na Abuja

- Wasu 'yan ta'adda sun kai hari wani gidan marayu a babban birnin tarayya Abuja

- 'Yan ta'addan sun sace mutane 8 daga gidan marayun da kuma mutum 3 daga makotansu

- Shugaban yankin ya tabbatar da fauwar hakan, hakanan 'yan sanda sun tabbatar

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu satar mutane ne sun mamaye gidan marayu na Rachael da ke gaban UBE Junior Secondary School a Naharati, Abaji Area Council, Abuja, suka sace marayu bakwai, ciki har da mai gadin gidan da ke yankin.

Daily Trust ta gano cewa mutane uku, wadanda suka hada da matan gida biyu, Rukaiyyat Salihu, Suwaiba Momoh da Momoh Jomih, wadanda ke zaune a bayan gidan marayun su ma masu garkuwar sun sace su.

Sunayen marayun da aka sace sun hada da Elizabeth Andrew, Dayo Udeh, Jacob Ukpas, Melody Ijeh, Benard Itim, Issac Mathew da Laruba Emmanuel da kuma mai tsaron gidan, Joseph Mathew.

KU KARANTA: Masu kiwon kaji na rokon Buhari kan shigo da masara da waken soya daga kasar waje

‘Yan Bindiga sun sace marayu 8 da wasu 3 a gidan marayu na Abuja
‘Yan Bindiga sun sace marayu 8 da wasu 3 a gidan marayu na Abuja Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Wani mazaunin yankin wanda ya bukaci a sakaya sunansaya ce: "A zahiri, sun shigo ne, da yawansu dauke da muggan makamai, duk da cewa ba su yi harbi ba yayin da suke gudanar da barnar a natse kafin su zarce zuwa gidajen makwabta," in ji shi.

Ya ce 'yan bindigar sun sami damar shiga ta babbar kofar.

Wani wanda abin ya rutsa dashi, Mohammed Nurudeen, wanda ‘yan bindigar suka sace matar sa, Rukaiyyat Salihu, ya ce: "Ina barci lokacin da suka zo suka yi barazanar harbi na idan na ki bude musu kofa,"

Ya bayyana cewa: "Da na ki amincewa har sai da suka tilasta kofar ta bude suka shiga cikin dakin suka yi awun gaba da matata," in ji shi.

Shugaban karamar hukumar, Alhaji Abdulrahman Ajiya, ya tabbatar da faruwar lamarin ta hanyar hira da wakilin Daily Trust ta wayar tarho, inda ya ce ya sanar da jami’an tsaro da abin ya shafa.

Lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda na babban birnin tarayya, ASP Maryam Yusuf, ta tabbatar da faruwar lamarin, duk da cewa ta yi ikirarin cewa mutane shida ne aka sace yayin da mutum daya ya samu kubuta.

KU KARANTA: An gurfanar da wani dan Najeriya a kasar Ghana da zargin satar tayal

A wani labarin, Wasu ‘yan bindiga da suka sace shugaban karamar hukumar Ardo-Kola a jihar Taraba, Salihu Dovo, sun kashe shi da sanyin safiyar Lahadi, in ji mazauna yankin.

Sun ce masu garkuwar sun kira wani jami'in karamar hukumar don sanar da su cewa sun kashe Mista Dovo sannan kuma sun ambaci inda za su samu gawar tasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.