'Yan Adawa Sun Gana da Atiku da Obi domin Samar da Dan Takara 1
- Shugabannin jam'iyyun adawa shida na ƙasa sun gudanar da tattaunawa da 'yan takarar shugaban ƙasarsu domin samun matsaya guda gabanin zaɓen 2027
- Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC na shiyyar Arewa maso Yamma, Salihu Lukman, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar
- Matakin na zuwa ne sakamakon ƙoƙarin aiwatar da shawarwarin da aka cimma a taron shugabannin adawa na G-100 domin gina adawa mai ƙarfi gabanin zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Shugabanni da sakatororin gudanarwa na jam'iyyun adawa shida sun fara tuntubar 'yan takarar shugaban ƙasarsu domin fito da tsarin haɗaka na tsayawa takara a zaɓen 2027.
Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC na shiyyar Arewa maso Yamma, Salihu Lukman, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, inda ya ce har yanzu ana tsaka da gudanar da tattaunawar.

Source: Facebook
Punch ta rahoto cewa jam'iyyun da ke cikin wannan tsari sun haɗa da ADC, APM, NDC, SDP, PDP da kuma PRP.
'Yan adawa da aka zauna da su
Lukman ya bayyana cewa mutanen da aka tuntuba ya zuwa yanzu sun haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar (ADC), Gwamnan Jihar Oyo Seyi Makinde (APM).
Ya ce sauran sun hada da tsohon gwamnan Jihar Anambra Peter Obi (NDC), Prince Adewole Adebayo (SDP) da kuma tsohon gwamnan Jihar Cross River Donald Duke (PRP).
Daily Trust ta rahoto ya ce:
"Tattaunawar tana nan tana tafiya. Saduwa ta gaba za ta gina ne a kan matsaya ta taron G-100 da kuma ƙoƙarin fito da tsarin adawa mai karfi, wanda zai iya aiki tare domin muradun ƙasa."
Batun tsayar da dan takara
A cewar Lukman, tattaunawar tana da nufin fito da wani tsari na haɗin gwiwa, gano muhimman abubuwan da jam'iyyun suka yi tarayya a kai, da kuma matakan da za a ɗauka domin ciyar da tsarin siyasa gaba.

Kara karanta wannan
An kwance wa Kwankwaso zani a kasuwa da NNPP ta fadi shirinta kan babban zaben 2027
Kodan da yake ba a kai ga cimma matsaya a kan 'dan takara guda ɗaya ba har yanzu, wannan mataki na nuni da haɗin kan da jam'iyyun adawar ke ƙoƙarin yi domin ƙalubalantar jam'iyyar APC mai mulki da shugaba Bola Tinubu.

Source: Facebook
Atiku da Obi, waɗanda suka zo na biyu da na uku a zaɓen 2023, na gaba-gaba wajen jan ragamar wannan harka ta haɗaka, duk da cewa har yanzu akwai rarrabuwar kai kan yadda za a zaɓi ɗan takara guda.
Atiku ya bukacia karbi PVC
A wani labarin, mun ruwaito cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya soki hauhawar farashin kayayyaki da rashin tsaro a ƙasar, inda ya yi alƙawarin kyautata rayuwa idan aka ba shi dama.
Atiku ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a ranar Laraba, inda ya buƙaci 'yan Najeriya da su karɓi katin zaɓensu na dindindin gabanin zaɓe mai zuwa.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce 'yan Najeriya na fuskantar matsin lamba na tattalin arziƙi da matsalar tsaro, inda ya ƙara da cewa ya san radadin da mutane ke ciki.
Asali: Legit.ng
