Da Dumi-Dumi: 'Yan bindiga sun kashe shugaban wata karamar hukuma a Taraba
- 'Yan ta'adda sun kashe shugaban wata karamar hukuma a jihar Taraba
- A baya sun dira gidan shugaban karamar hukumar suka sace shi kafin daga bisani suka kashe shi
- Wasu mutane suna zargin hayar 'yan fashin a ka yi domin aikata wannan mummunan ta'asa
Wasu ‘yan bindiga da suka sace shugaban karamar hukumar Ardo-Kola a jihar Taraba, Salihu Dovo, sun kashe shi da sanyin safiyar Lahadi, in ji mazauna yankin.
Sun ce masu garkuwar sun kira wani jami'in karamar hukumar don sanar da su cewa sun kashe Mista Dovo sannan kuma sun ambaci inda za su samu gawar tasa.
Wasu daga cikin al’ummar yankin suna zargin wadanda suka sace shi hayarsu aka yi don su kashe shi.
"Sun kira wani jami'in karamar hukumar don sanar da shi kisan, inda suka ce su je su nemi gawar sa a cikin daji," in ji daya daga cikin majiyar Premium Times.
KU KARANTA: Wasu manyan jam'iyyar APC 12 na son matasa su ja ragamar jam'iyyar
“Membobin yankin sun shiga daji suka fara neman gawar sa kuma an gano ba da dadewa ba. Ana daukar gawar zuwa gari yanzu,” majiyar ta ce.
‘Yan bindigar sun kutsa kai gidan Mista Dovo da ke Sabon Gari, Jalingo da misalin karfe 1 na rana.An dauke shi ne yayin da ake zargin yin garkuwa da shi kafin maharan suka kashe shi.
Lokacin da aka tuntube shi, kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, David Misal, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an kama wanda ake zargi.
”Kamar yadda nake magana da ku yanzu, an ijiye gawar sa a asibiti."
Mista Misal, Mataimakin Sufeto Janar na 'yan sanda, ya ce "Jami'an' yan sanda sun fara aiki kamar yadda aka kama wani da ake zargi".
KU KARANTA: Gwamnatin jihar Kano za ta nada jami'an ladabtarwa na COVID-19
A wani labarin, 'Yan bindiga sun sake kashe mutane takwas a kauyukan Dutsin Gari da Rayau da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara a wani sabon hari.
Wani shaidar gani da ido, Malam Ibro Mamman ya zanta da wakilin The Punch ya ce ‘yan fashin a kan babura sun mamaye kauyen Dutsin Gari a daren jiya da niyyar yin garkuwa da wasu mutane amma mazauna garin sun fuskance su gaba daya.
A cewarsa, mazauna kauyen sun gwabza da 'yan fashin a wani kazamin fada wanda ya dauki tsawon awanni.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng