Ahmed Musa zai koma kungiyar kwallon kafa ta West Brom

Ahmed Musa zai koma kungiyar kwallon kafa ta West Brom

- Shahararren dan wasan kwallon kafan Najeriya Ahmad Musa zai koma wata sabuwar kulob

- Dan wasan kasancewar ya kwan biyu a kasa, an bayyana zai koma West Brom na wani dan lokaci

- Ahmad Musa shine kaftin din kungiyar kwallon kafa na Najeriya wato Super Eagles

Kaftin din Super Eagles Ahmed Musa na shirin komawa kungiyar kwallon kafa ta West Bromwich Albion masu buga Premier a kan yarjejeniyar wani gajeren lokaci.

Dan wasan mai shekaru 28 bai kasance a wata kungiyar kwallon kafa ba tun lokacin da ya bar Al Nassr a cikin Oktoba 2020, The Punch ta ruwaito.

A cewar Daily Mail, Baggies sun nemi bizar dan wasan kuma sun shirya don duba lafiyarshi a ranar Laraba.

KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe jami’in 'yan sanda sun saci bindiga AK-47 a garin Kafanchan

Ahmed Musa zai koma kungiyar kwallon kafa ta West Brom
Ahmed Musa zai koma kungiyar kwallon kafa ta West Brom Hoto: Sports24
Asali: UGC

Ahmad Musa ya buga wa Najeriya wasanni sau 95, aikin Musa ya tsaya tun lokacin da ya bar CSKA Moscow a shekarar 2016. Kasancewa ya ci kwallaye 55 a wasanni 167 da ya buga wa Russia, ya koma Leicester City a bazarar shekarar.

Abubuwa ba su yi nasara ba a filin wasa na King Power, saboda dan Musa ya buga wasanni bakwai ne kawai a farawa 21.

Ya shiga bayan Foxes sun yi ikirarin lashe gasar Firimiya kuma suna fatan kasancewa cikin wani abu na musamman da kungiyar.

Amma an bada Musa haya zuwa CSKA na rabin sashe na biyu a zangon 2017/18.

Daga nan aka siyar da shi ga Al Nassr a cikin Janairun 2019 kuma ya buga wasanni 62 a duk gasa kafin a sake shi.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya tana sake ginawa, ta gyara hanyoyi 43 a manyan makarantu

A wani labarin, Mai horas da ‘yan wasan kungiyar Real Madrid, Zinedine Zidane, ya kamu da COVID-19 kamar yadda kulob din ya bada sanarwa a ranar Juma’ar nan.

Gwajin da aka yi ya tabbatar da cewa Zinedine Zidane ya na dauke da kwayar cutar COVID-19.

“Kungiyar kwallon kafan Real Madrid ya na sanar da cewa gwaji ya nuna mai horas da ‘yan wasanmu, Zinedine Zidane, ya kamu da cutar COVID-19.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel