Wasu manyan jam'iyyar APC 12 na son matasa su ja ragamar jam'iyyar
- Wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun bayyana son canji da suke son kawowa cikin jam'iyyar
- Jiga-jigan sun nuna sunason shigo da matasa masu jini a jika a jagorancin jam'iyyar APC
- Hakazalika sun bayyana ba sa son sake wasu wadada suka taba rike matsayi jagorancin jam'iyyar
Wata kungiyar gamayya da ta kunshi gwamnoni 12, shugabanni masu fada a ji, Sanatoci da mambobin majalisar wakilai ta fito a cikin APC gabanin babban taron jam’iyyar na kasa a watan Yuni.
Rahoto ya tattaro cewa, manufar gamayyar, shine a nada sabon shugaban jam'iyyar, The Nation ta ruwaito.
An ce gwamnonin da sauran masu ruwa da tsaki cikin lamarin su ke adawa da duk wanda ya girmi shekaru 65 yana jagorantar jam’iyyar.
KU KARANTA: 'Yan damfara da sunan COVID-19 sun bayyana a birnin Abuja, FCTA
Har ila yau, gamayyar kungiyoyin na neman fahimtar shugabannin jam’iyyar ta APC da su amince da shugabancin jam’iyyar na shiyyar Arewa ta Tsakiya saboda duka Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma suna da nasu kason na ofisoshin siyasa.
An gano cewa sun fara neman sayan manyan shugabannin APC da masu ruwa da tsaki kan bukatar samari matasa da za su jagoranci jam’iyyar.
A cewar wata majiya mai tushe, gamayyar nan ba da dadewa ba za ta tuntubi Shugaba Muhammadu Buhari kan tsarin shugabancin ta na APC.
Majiyar ta ce: “Muna kafa hadaka don aiwatar da gyare-gyare mai dorewa a cikin APC. Ba za mu bar gwamnoni su kadai su jagoranci yunƙurin kawo canje-canje a cikin jam'iyyarmu ba.
“Mun hadu sau biyu kuma mun yanke shawarar kafa kungiyar Movement for New Generation of Leadership a APC.
"Ba mu son kowane dan takara ko dan takarar da ya taba zama gwamna, mataimakin gwamna, minista, sakatare na dindindin, jakada, babban darakta ko Shugaba na kowane MDA ya jagoranci APC.
“Mun yi imanin cewa wadanda suka rike mukamai a baya ya kamata su koma baya. Muna son gwada sabon abu a cikin APC."
KU KARANTA: Fulani na da 'yancin zama a Ondo, in ji sarakunan gargajiya a Ondo
A wani labarin, Ba da daɗewa ba za a ƙaddamar da wata jam'iyya mai ban tsoro, in ji tsohon Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, a ranar Litinin, The Nation ta ruwaito.
Ya ce sabuwar jam'iyyar za ta samar da wani abin dogaro na gaskiya ga jam'iyyar PDP da jam'iyyar APC mai mulki.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng