Bayan Dogon Bincike, An Gano Cutar da Ta Kashe Mutane 5 'Yan Gida 1 a Jihar Kano

Bayan Dogon Bincike, An Gano Cutar da Ta Kashe Mutane 5 'Yan Gida 1 a Jihar Kano

  • Hukumar Kula da Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC) ta tabbatar da cewa cuta mashako (diphtheria) ta yi ajalin yara biyar yan gida daya a Kumbotso
  • Yara shida daga iyali ɗaya ne suka kamu da cutar, inda mutum biyar suka mutu sakamakon kai su asibiti a makare
  • Hukumar ta buƙaci iyaye da masu kula da yara su tabbatar da yi wa yara rigakafi tare da garzayawa asibiti da zarar an ga alamun rashin lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Hukumar Yaki da Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC) ta tabbatar da ceea cutar mashako watau diphtheria ce ta yi sadanin mutuwar yara biyar yan gida daya.

Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa yara biyar yan gida daya a unguwar Danbare, Layin Dutse, Ƙaramar Hukumar Kumbotso ta Jihar Kano sun mutu sakamakon wata cuta da ake zargin mashako ce.

Kara karanta wannan

Kwana ya ƙare: Tsohon Shugaban FRSC ta Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

Kano.
Taswirar jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Shugaban hukumar KNCDC, Farfesa Muhammad Adamu-Abbas, ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

KNCDC ta kammala bincike a Kano

Muhammad, ya tabbatar da mutuwar yaran bisa bayanan alamomin cutar da kuma binciken gawarwaki ta hanyar tattaunawa da yan uwan mamatan.

Ya danganta mutuwar yaran da kai su cibiyar lafiya a makare da kuma rashin karɓar allurar rigakafin mashako ko kaɗan. Ya ce shekarun yaran da suka mutu sun kasance daga shekara ɗaya zuwa 13.

“Binciken ya tabbatar da cewa yara shida daga iyali ɗaya ne suka kamu da cutar. Abin takaici, biyar daga cikinsu sun mutu saboda an kai su asibiti a makare.
“An kwantar da yarinya ta shida, Ummahabila Ibrahim, mai shekara huɗu, a asibiti a ranar 1 ga Oktoba, 2026, bayan ta kamu da cutar diphtheria mai sauƙi.
"An sallame ta a ranar 4 ga Oktoba, 2026. Binciken da aka sake yi a ranar 12 ga Oktoba, 2026, ya tabbatar da cewa ta warke sarai kuma tana cikin ƙoshin lafiya," in ji Mohammed.

Kara karanta wannan

Pantami: INEC ta yi magana kan 'yan takara a Gombe, Kano da jihohi 4

Abin da binciken ciwon ya gano

A cewarsa, binciken lafiyar yaran ya nuna alamun cutar diphtheria mai tsanani, ƙarancin ƙwayoyin jinin da ke taimakawa wajen daskarewar jini, ƙarancin jini, lalacewar jijiyoyo da kuma haɗarin toshewar hanyar numfashi ta sama.

Ya kuma bayyana cewa binciken ya nuna yara uku daga cikin biyar da suka mutu ba su taɓa karɓar ko da allurar rigakafi guda ɗaya ba.

“Mahaifiyar yaran ta bayyana cewa an yi wa yara biyu rigakafi, amma babu katunan da ke tabbatar da karɓar allurar rigakafim saboda an ce sun ɓace lokacin da iyalin suka canza gida,” in ji shi.
diphtheria
Yadda ake yi wa kananan yara allurar rigakafin kamuwa da cutar mashako Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Shugaban KNCDC ya yi kira ga iyaye da masu kula da yara da su garzaya cibiyar kula da lafiya matakin farko mafi kusa domin kammala allurar rigakafin da yaran suka rasa.

Jihohin da cutar mashako ta fi yaduwa

Kun ji cewa hukumar NCDC ta bayyana cewa galibin wadanda suka kamu da cutar mashako watau diphtheria ba su yi rigakafi ba.

Ta kuma jero jihohi takwas da cutar ta fi yaduwa, wadanda ta ce 98% na masu dauke da wannan cuta suna wadannan jihohi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262