Buhari ya ba da umarnin sakin $20m ga ECOWAS don magance ta'addanci

Buhari ya ba da umarnin sakin $20m ga ECOWAS don magance ta'addanci

- Shugaban kasar Najeriya ya bada umarnin sake makudan kudade wa ECOWAS don magance ta'addanci

- Shugaban ya kuma nemi a sake tsarin shugabancin kungiyar don gudanarwa mai inganci

- Shugaba Buhari kuma jaddada cewa sake fasalin kungiyar zai taimaka wajen inganta shugabancin kungiyar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin sakin dala miliyan 20 nan take, wanda Nijeriya ta yi alkawarin bayarwa a baya ga asusun ajiyar shirin ECOWAS na yaki da ta'addanci a fadin yankin, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban ya sanar da wannan umarni ne a yayin wata gabatarwa ga taron kara wa juna sani karo na 58 na Shugabannin kasashe da gwamnatocin ECOWAS, a Abuja, ranar Asabar.

”Mun riga mun bayar da umarnin a tura nan da nan na dala miliyan 20 da Najeriya ta yi alkawari zuwa asusun ajiyar shirin na ECOWAS don yaki da ta’addanci,

"Yayin da za a raba dala miliyan 80 don yaki da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas da 'yan fashi a Arewa maso Yammacin Najeriya na shekara ta 2020.

"Mun kuma kudura aniyar ganin mun cika alkawurranmu na ragowar lokacin aikin," in ji shugaba Buhari.

KU KARANTA: Wasu manyan jam'iyyar APC 12 na son matasa su ja ragamar jam'iyyar

Buhari ya ba da umarnin sakin $20m ga ECOWAS don magance ta'addanci
Buhari ya ba da umarnin sakin $20m ga ECOWAS don magance ta'addanci Hoto: Arise News
Asali: UGC

Shugaban ya kuma bayar da shawarar a sake fasalin ECOWAS, yana mai cewa kungiyar tana bukatar daidaita tsarin gudanarwarta don daidaituwa da abubuwan da ke faruwa a yanzu.

"Yanayin da ECOWAS ta nada mutane 23, kuma 13 daga cikinsu Kwamishinoni ne na wannan Kwamitin ba zai yiwu ba", in ji shugaba.

Yayi wannan furici bw a lokacin da yake gabatar da jawabi ga taron kara wa juna sani karo na 58 na Shugabannin Kasashe da Gwamnatocin ECOWAS, a Abuja, a ranar Asabar.

Ya kuma jaddada cewa akwai bukatar samun shugabanci mai karko a cikin ECOWAS, don inganta kwazon kungiyar da kuma inganta ta.

Ya kara da cewa sake fasalin zai kawar da sakewa da kuma takaddama tsakanin manyan mukamai da aka nada, tare da rage ma'aikata da kuma samaR da kudaden da za a iya samu don aiwatar da ayyukan kungiyar.

KU KARANTA: Gwamnatin jihar Kano za ta nada jami'an ladabtarwa na COVID-19

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya sake jaddada bukatar kasashen makwabta su kasance masu kiyaye muradun juna a koda yaushe, yana mai cewa dorewar juna ya dogara da juna, Vanugard News ta ruwaito.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne lokacin da yake karbar bakuncin shugaban kasar Benin, Patrice Talon, wanda ya kai ziyarar gani da ido a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.