Ya kamata a hukunta 'yan leken asirin 'yan fashi daidai da 'yan fashi - Bello

Ya kamata a hukunta 'yan leken asirin 'yan fashi daidai da 'yan fashi - Bello

- Gwamna jihar Neja ya rantsar da sabuwar babbar alkalin jihar a zauren majalisa a gidan gwamnati

- Gwamnan ya bukaci alkalin da majalisar jiha da su hannu wajen hukunta masu bai wa 'yan fashi bayanai

- Gwamnan ya siffanta aikin masu ba da bayanan da yin fashi matsayin abu daya

Gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya bayyana cewa masu ba da bayanai ga 'yan fashi na da hadari kamar 'yan fashi sannan ya nemi a yi musu irin hukuncin da 'yan fashi da masu satar mutane suke amsa idan aka kama su.

Ya fadi haka ne bayan rantsar da sabuwar babbar alkalin jihar, Mai shari’a Aisha Bwari, a zauren majalisar a gidan gwamnati. Ya lura cewa in ba masu ba da bayanan ba, 'yan fashin ba za su iya aiwatar da ayyukansu ba, Daily Trust ta ruwaito.

Ya bukaci bangaren shari’a da na majalisa da su fito da hukunci mai tsauri ga wadanda ke da hannu a cikin wadannan ayyukan, musamman masu ba da bayanan, yana mai cewa akwai bukatar a kafa misali ga wadanda suke da hannu a cikin wadannan ayyukan.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun cafke wani dan damfara mai ikirarin shi jami'in EFCC ne a Abuja

Ya kamata a hukunta 'yan leken asirin 'yan fashi daidai da 'yan fashi - Bello
Ya kamata a hukunta 'yan leken asirin 'yan fashi daidai da 'yan fashi - Bello Hoto: Daily Trust
Source: UGC

Mai shari’a Bwari ta yi alkawarin cewa za a samu sauyi a bangaren shari’a, yana mai cewa ya kamata a hada dukkan hannaye don tabbatar da hakan.

Ta kuma bayar da tabbacin cewa bangaren shari’a zai yi aiki tare tare da bangaren zartarwa da na majalisa don aiwatar da dokoki don amfanin jihar.

KU KARANTA: Gwamnatin jihar Kano za ta nada jami'an ladabtarwa na COVID-19

A wani labarin, 'Yan bindiga sun sake kashe mutane takwas a kauyukan Dutsin Gari da Rayau da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara a wani sabon hari.

Wani shaidar gani da ido, Malam Ibro Mamman ya zanta da wakilin The Punch ya ce ‘yan fashin a kan babura sun mamaye kauyen Dutsin Gari a daren jiya da niyyar yin garkuwa da wasu mutane amma mazauna garin sun fuskance su gaba daya.

A cewarsa, mazauna kauyen sun gwabza da 'yan fashin a wani kazamin fada wanda ya dauki tsawon awanni.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel