Masu kiwon kaji na rokon Buhari kan shigo da masara da waken soya daga kasar waje

Masu kiwon kaji na rokon Buhari kan shigo da masara da waken soya daga kasar waje

- Shugaban wata kungiyar masu kiwon kaji ya bukaci gwamnati da tallafa wajen shigo da masara da waken soya

- Yayi kira ga gwamnati da ta hana fitar da nau'ukan waken soya da masara a kasar

- Ya kuma bayyana irin asara da kuma hauhauwar farashi da kasauwar ke fuskanta

Dakta Olalekan Odunsi, babban sakatare-janar na kudu maso yamma na kungiyar masu kiwon kaji a Najeriya (PAN), ya yi kira ga gwamnati da ta saukaka shigo da masarar dabbobi da waken soya, Daily Trust ta ruwaito.

Odunsi yace shigo da kaya daga waje zai ceci masana'antar kaji daga durkushewa.

Ya ce shigo da masara cikin gaggawa zai ciyar da sama da kajin kwai miliyan 50, kajin nama miliyan 100, masu shayarwa miliyan 1 da sauran nau'ikan kiwon kaji har zuwa lokacin girbi na gaba.

Ya kuma bukaci gwamnati da ta aiwatar da dokar hana fitar da waken soya, da sauran nau'ukan abinci kasashen waje.

KU KARANTA: Wasu manyan jam'iyyar APC 12 na son matasa su ja ragamar jam'iyyar

Masu kiwon kaji na rokon a shigo da masara da waken soya don kiwon kaji
Masu kiwon kaji na rokon a shigo da masara da waken soya don kiwon kaji Hoto: Food Business News
Asali: UGC

Ya bukaci gwamnoni a yankin da su himmatu wajen karfafa noman masara kamar yadda suka yi na shinkafa.

Ya ce tsananin karancin abinci da hau-hawar farashin waken soya da masara zai yi barazanar karin ayyuka miliyan biyar a cikin gajeren lokaci idan gwamnati ba ta sa baki ba.

“A yau, ana sayar da masara a N210, 000/MT a yawancin jihohin Kudu maso Yamma, waken soya N240, 000/MT.

“Saboda mahimmancin waɗannan abubuwa biyu, farashin abincin kaji ya ci gaba da ƙaruwa daga N2750 zuwa N3000 a watan Afrilu N2020 zuwa N4850 zuwa N5300 a yanzu.

"A watan Disamba, mafi yawan manoma ba sa iya sayar da kajin namansu saboda farashin abin da yake samarwa ya fi wanda talakawan Najeriya za su iya saya.

"A yanzu haka, kwai farashinsa ya kokarin haura N1, 300." in ji shi.

KU KARANTA: Gwamnatin jihar Kano za ta nada jami'an ladabtarwa na COVID-19

A wani labarin, Mista Ezra Amos, mai shekara 70 kuma tsohon ma'aikacin gwamnati daga yankin Dadin Kowa na Jihar Gombe ya ce ya samu sama da Naira miliyan 3 daga noman kifi a shekarar 2020.

Amos, wanda ya yi magana a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Dadin Kowa, karamar Hukumar Yamaltu-Deba, ranar Laraba, ya ce noman kifi yana biyan bukatunsa a matsayinsa na ma’aikacin gwamnati da ya yi ritaya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel