An gurfanar da wani dan Najeriya a kasar Ghana da zargin satar tayal
- Jami'an 'yan sanda a kasar Ghana sun gurfanar da wani dan Najeriya a kotu da zargin sace tayal
- Matashin an kama shi ne a yayin kulle wani gidan ajiya da a ke zargin ya shiga ya saci tayal da yakai darajar $50,000
- Sai dai matashin ya musanta zargin da a ke masa, kotu ta daga karar zuwa wani lokaci don yanke hukunci
Felix Gabriel, wani matashi dan shekara 32 dan Najeriya, ya bayyana a gaban Kotun Da’irar Accra kan zargin shiga cikin wani dakin ajiya da satar tayal din da kudinsu ya kai $50,000.00.
An ce Gabriel ya hada baki da wasu, suka kutsa kai cikin dakin ajiyar kayan sannan suka loda kayan a wasu manyan motoci zuwa wani wurin da ba a sani ba, in ji rahoton Ghanaweb.
Ana tuhumarsa da sata, sai dai Gabriel ya musanta aikata laifin, Sahara Reporters ta ruwaito.
Kotun karkashin jagorancin Misis Evelyn Asamoah, ta bayar da belin Gabriel a kan kudi GHC450,000.00 tare da mutane uku da za su tsaya masa.
KU KARANTA: Gwamnatin jihar Kano za ta nada jami'an ladabtarwa na COVID-19
Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Fabrairu domin gudanar da zaman Gudanar da Shari'a.
Babban Sufeto Emmanuel Haligah ya ruwaito cewa, mai shigar da karar, Nii Oten Granaky I, kimanin watanni biyu da suka gabata, ya kwashe tarin tayal din da darajarsu ta kai $50,000.00 (ko kuma cedi kwatankwacin GHC340,000.00) a kulle da mabuɗi.
An kama wanda ake zargin tare da mika shi ga ‘yan sanda.
Ya ce yayin bincike, Gabriel ya amince da laifin a cikin bayanin nasa. Ya ce ya ambaci Bright da Mohammed da wasu mutum biyu, a yanzu haka, a matsayin mutanen da suka shigo da motocin KIA don kwashe tayal din.
Ya kara da cewa wadanda ake zargin sun sake sabon makulli don kulle dakin ajiyar kuma a cikin hakan, aka kama su.
Ya ce, "Wanda ake tuhumar, duk da haka, ba zai iya jagorantar 'yan sanda su kama wadanda suke tare da shi ba."
KU KARANTA: Wasu manyan jam'iyyar APC 12 na son matasa su ja ragamar jam'iyyar
A wani labarin, Jami’an ‘yan sanda da ke reshen Mabushi na babban ofishin 'yan sanda na Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja sun cafke wani Mohammed Abdulrahman da ake zargi da yin karyar a matsayin Sufeto Janar na ‘yan sanda.
Hakazalika ana zarginsa da ikirarin cewa shi jami’in Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFCC, Nigerian Tribune ta ruwaito.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng