SERAP ta bukaci bayani kan N5,000 da za a bai wa 'yan Najeriya
- SERAP ta bukaci Minista Sadiya Umar Faruq ta bada bayanin yadda aka tsara bai wa 'yan Najeriya miliyan 24.3 N5,000 kowannensu
- Kungiyar ta bukaci bayanin ne don a fito da gaskiyar lamarin balo-balo wa al'umma
- Kungiyar ta kuma shawarci ministar da ta hada kai da EFCC da ICPC wajen gudanar da binciken
Kungiyar Kare Hakkin Tattalin Arziƙi da Ayyukan Amana (SERAP) ta bukaci Ministan Harkokin Jin Kai da Ci Gaban Jama’a, Hajia Sadiya Umar Farouq, ta “buga bayanan yadda ake shirin biyan Naira biliyan 739 zuwa ga miliyan 24.3 na talakawa na tsawon watanni shida”.
Kungiyar ta nemi a ba da cikakkun bayanan ne a kan takardar ‘Yancin Ba da Bayani (FoI), a ranar 23 ga Janairun 2021, dauke da sa hannun Mataimakin Darakta Kolawole Oluwadare.
SERAP ta kuma bukaci ministar da “ta yi bayanin dalilin da ya sa aka bada N5,000 wa mutane miliyan 24.3 'yan Nijeriya talakawa," The Nation ta ruwaito.
KU KARANTA: Masu kiwon kaji na rokon Buhari kan shigo da masara da waken soya daga kasar waje
A makon da ya gabata, Umar Farouq ta sanar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta biya kimanin ‘yan Nijeriya miliyan 24.3 matalauta N5,000 ga kowannensu na tsawon watanni shida “don samar da taimako ga wadanda suka talauce da cutar ta COVID-19 ”.
Kungiyar ta ce: "Buga bayanan wadanda suka ci gajiyar shirin da kuma ka'idojin tantancewar da kuma shirin biyan kudin na tsawon watanni shida zai inganta gaskiya da rikon amana tare da kawar da barazanar rashin tsari da karkatar da kudaden jama'a."
Kungiyar ta shawarci Umar Farouq da “ta gayyaci Hukumar Yaki da Cin Hanci da yi wa Tattalin Arziki zagon kasa (EFCC) da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuffuka Masu Alaka (ICPC) da su hada hannu tare da bin diddigin kudaden."
KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe jami’in 'yan sanda sun saci bindiga AK-47 a garin Kafanchan
A wani labarin, Masu cin gajiyar N-Power, wadanda suka kammala shirin aikin na shekaru biyu, yanzu za su sami damar samun aikin dindindin ko damar kasuwanci, in ji Gwamnatin Tarayya.
Wannan wani bangare ne na sabuwar kokarin gwamnati kan fita daga tsarin N-power.
Tsarin an yi shine ga dukkan 'yan tsarin A da B na shirin N-Power.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng