Akwai Matsala: Tanubu ba Zai Iya zuwa Kamfe a Wasu Jihohin Najeriya ba
- Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa ba zai iya zagaya dukkan jihohin Najeriya yayin yakin neman zabensa gabanin zaben 2027 ba
- Tinubu ya ce Najeriya na buƙatar kulawarsa fiye da kowane lokaci, don haka ba zai iya bin tawagar kamfen zuwa dukkan jihohi da ƙananan hukumomi ba
- Ya ƙaddamar da kwamitin kamfen ɗin shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya bayyana cewa mai yiwuwa ba zai zagaya dukkan jihohin ƙasar yayin yakin neman sake zaɓensa a babban zaɓen 2027 ba.
Shugaban ya bayyana hakan ne a jawabinsa yayin ƙaddamar da kwamitin kamfen ɗin shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a fadar shugaban ƙasa, Aso Rock, Abuja, ranar Laraba.

Source: Facebook
A rahoton Daily Trust, Tinubu ya ce an shawarce shi da kada ya bari ayyukan kamfen su ɗauke hankalinsa daga gudanar da mulkin ƙasar, yana mai cewa Najeriya na buƙatar kulawarsa a halin yanzu.
Da yake jawabi jim kaɗan bayan ƙaddamar da kwamitin kamfen, Tinubu ya bayyana cewa nauyin da ke kansa na shugabancin ƙasa ba zai ba shi damar halartar kowane gangamin hakin neman zabe ba.
Tinubu ba zai iya zuwa kowace jiha ba
Duk da cewa ya yi alƙawarin ware lokaci domin tattaunawa kai tsaye da ’yan Najeriya, shugaban ya shaida wa kwamitin kamfen da Sanata Abdulaziz Yari ke jagoranta cewa ba zai iya zuwa dukkan jihohi da ƙananan hukumomi ba.
“Kun gargaɗe ni kuma kun roƙe ni da kada in bari wahalhalun kamfen su ɗauke hankalina daga gudanar da mulki. Na ji shawarar ku, kuma na amince da wannan matsaya taku gaba ɗaya.
“Najeriya na buƙatar kulawa sosai a yanzu fiye da kowane lokaci. Nauyin da ke kan wannan ofishi ba ya tsayawa.
“Duk da haka, zan ware lokaci domin tattaunawa kai tsaye da ’yan Najeriya, yayin da kuke jagorantar kamfen a jihohi da ƙananan hukumomi. Saboda haka, za ku yi haƙuri idan ba zan iya zuwa tare da ku a dukkan wuraren ba.”

Kara karanta wannan
Magana ta fito daga bakin minista, an ji adadin shekarun da Tinubu ke buƙata a kan mulki
- Bola Tinubu.
Tinubu ya nuna muhimmancin kwamitin
Tinubu ya bayyana cewa ƙaddamar da kwamitin kamfen ba wani taro kawai ba ne, illa sabunta alƙawarin da suka ɗauka ga ’yan Najeriya da kuma nauyin da ke kan jam’iyyar mai mulki.
Shugaban ya kara da cewa
“Ba kawai mun taru ne domin ƙaddamar da kamfe ba. Mun taru ne domin sabunta alƙawari, alƙawari ga al’ummar Najeriya da kuma nauyin da suka ɗora mana a matsayin jam’iyyar da ke mulkin ƙasar.”
Ya ƙara da cewa ana sa ran kwamitin zai isar da hangen nesan gwamnatin, nasarorin da ta samu da kuma shirye-shiryenta ga masu zaɓe a faɗin ƙasar.
Karin bayani na tafe...
Asali: Legit.ng
