'Yan bautar kasa 13 sun kamu da COVID-19 a sansanin NYSC
- An samu karuwar adadin wadanda suka kamu da cutar Korona a jihar Kuros Riba
- Kwamishinan lafiyar jihar ta bayyana shigowar 'yan bautar kasa ne ya kara sa hau-hauwar adadin
- Jihar zuwa ranar 24 ga watan Janairu, tana da adadin wadanda suka kamu da Korona mutum 189
A ranar Lahadin da ta gabata ne Jihar Kuros Riba ta kara samun mutane 20 da suka kamu da cutar COVID-19, kuma mafi yawa tun bayyanar Korona a jihar, Premium Times ta ruwaito.
Kafin wannan, jihar ta ci gaba da kasancewa a kasan tebur tun bayan barkewar cutar Coronavirus a Najeriya.
Adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a jihar yanzu 189 ne ya zuwa ranar 24 ga Janairu, a cewar bayanai daga Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya.
KU KARANTA: Fastocin kamfen din shugaban kasa na Wike sun bayyana a Abuja
Kwamishiniyar lafiya a jihar Kuros Riba, Betta Edu, ta ce yawan kamuwa da cutar da aka yi a jihar kwanan nan saboda ‘yan bautar kasa da suka shigo jihar ne.
“Muna da mutanen da suka shigo don NYSC, kusan 13 daga cikinsu sun kamu. Don haka, waɗannan mutane ne da suka shigo zuwa jiharmu daga wasu jihohin."
Misis Edu ta ce, “Sauran su ne mutanen da ke zaune a jihar,” kamar yadda Misis Edu ta fada wa Premium Times ranar Litinin.
Kuros Riba, kafin yanzu, tana da dakunan gwaje-gwaje biyu don gwajin COVID-19 - Lawrence Henshaw Memorial Reference Lab da kuma asibitin koyarwa na Jami'ar Calabar (UCTH).
KU KARANTA: El-Zakzaky da matarsa basu halarci shari’arsu da gwamnatin Kaduna ba
A wani labarin, Wata babbar gobara ta tashi a ranar Alhamis, a harabar kamfanin kera allurar kwayar cuta ta Serum ta Indiya, SII, a garin Pune na Indiya.
Gobarar ta fara ne da rana a yankin Manjari na harabar SII, babban jami’in kashe gobara na Pune, Prashant Ranpise ya fada. Ya kara da cewa an tura jami’an kashe gobara 15 zuwa wurin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng