‘Yan bindiga sun kashe jami’in 'yan sanda sun saci bindiga AK-47 a garin Kafanchan

‘Yan bindiga sun kashe jami’in 'yan sanda sun saci bindiga AK-47 a garin Kafanchan

- Wasu da ake zargi 'yan bindiga ne sun bindige wani dan sanda har lahira

- 'Yan bindigan sun kuma sace bindigar jami'in 'yan sandan kirar AK47

- Sun bindige shi ne a hanyarsa ta kai mai laifi zuwa hedkwatar 'yan sanda dake Jema'a a jihar Kaduna

An ba da rahoton cewa wasu ’yan bindiga sun bindige wani dan sanda har lahira da bindigarsa a daren Asabar a kan titin Jos a Kafanchan, hedkwatar karamar Hukumar Jema’a ta Jihar Kaduna.

Jami'in, mai suna Sajan John Auta, an ce yana aiki a Wonderland Hotel Annex da ke titin Ogbomosho, Kafanchan.

KU KARANTA: Buhari ya ba da umarnin sakin $20m ga ECOWAS don magance ta'addanci

‘Yan bindiga sun kashe jami’in 'yan sanda sun saci bindiga AK-47 a garin Kafanchan
‘Yan bindiga sun kashe jami’in 'yan sanda sun saci bindiga AK-47 a garin Kafanchan Hoto: Leadership Hausa
Source: UGC

Majiyar Daily Trust da ta nemi a sakaya sunanta ta ce wanda aka kashe din yana kai wanda ake zargi ne, wanda aka kama shi yana shan tabar wiwi zuwa hedkwatar rundunar.

Majiyar ta ce yayin da jami’in ke komawa hedikwatar ne aka harbe shi har lahira. Daga baya wasu jami’an ‘yan sanda da ke sintiri suka gano gawar tasa.

Lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige, ya ce ba shi da cikakken bayani game da lamarin amma ya yi alkawarin komawa ga wakilinmu.

KU KARANTA: Masu kiwon kaji na rokon Buhari kan shigo da masara da waken soya daga kasar waje

A wani labarin, Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu satar mutane ne sun mamaye gidan marayu na Rachael da ke gaban UBE Junior Secondary School a Naharati, Abaji Area Council, Abuja, suka sace marayu bakwai, ciki har da mai gadin gidan da ke yankin.

Daily Trust ta gano cewa mutane uku, wadanda suka hada da matan gida biyu, Rukaiyyat Salihu, Suwaiba Momoh da Momoh Jomih, wadanda ke zaune a bayan gidan marayun su ma masu garkuwar sun sace su.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel