Ciwon Kansa Ya Kama Fafaroma Leo, an Kwantar da Shi a Asibiti
- Paparoma Leo XIV ya kamu da cutar kansa a huhu, amma likitoci sun yi nasarar yi masa tiyata domin cire ɓangaren huhunsa na dama da cutar ta shafa
- Fadar Vatican ta bayyana cewa an yi wa Paparoma mai shekaru 71 tiyatar na tsawon mintuna 90 a ranar Talata a asibitin Gemelli da ke Rome
- Rahoton likitoci ya ce an yi nasarar tiyatar ba tare da samun wata matsala ba, kuma ana sa ran Paparoma zai shafe kusan mako guda a asibiti domin ya murmure
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma ƙwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Rome – Fadar Vatican ta tabbatar da cewa Fafaroma Leo XIV ya kamu da cutar daji a huhu, amma likitoci sun yi nasarar yi masa tiyata domin cire ɓangaren huhunsa na dama da cutar ta shafa.
Rahoto ya nuna cewa an yi wa Paparoma tiyatar ne a ranar Talata a asibitin Gemelli da ke birnin Rome na ƙasar Italiya, inda aikin ya ɗauki mintuna 90.

Source: Getty Images
A cikin sanarwar likitoci, BBC ta wallafa cewa Vatican ta ce an cire ƙasan ɓangaren huhun dama gaba ɗaya domin tabbatar da cewa an gudanar da aikin yadda ya kamata.
Sanarwar ta ƙara da cewa:
“An yi nasarar tiyatar ba tare da wata matsala ba. Bayan kammala aikin, Paparoma ya farka yadda ya kamata, sannan ya koma ɗakinsa bayan an ɗan tsare shi domin duba lafiyarsa.”
Yadda aka gano cutar Fafaroma
Vatican ta bayyana cewa an fara gano ƙurjin da ke huhun Fafaroma ne yayin wasu gwaje-gwajen lafiya na yau da kullum.
Bayan gudanar da ƙarin bincike, likitoci sun tabbatar cewa yana fama da cutar kansa ta huhu da ake kira pulmonary adenocarcinoma.
Sai dai Vatican ta ce alamun farko na gwaje-gwajen kafin tiyatar sun nuna yiwuwar kasancewar cutar, kuma an gano ta ne tun tana matakin farko.
A cewar bayanan da Fafaroma ya bayyana ranar Lahadi, ƙurjin da aka gano a huhunsa yana cikin wani wuri takamaimai, kuma likitoci sun ba da shawarar a cire shi domin kauce wa ƙarin matsala.

Kara karanta wannan
Magana ta fito, rundunar yan sanda ta bayyana dalilin kama tsohon gwamna a Najeriya
Vatican ta kuma jaddada cewa Fafaroma bai nuna alamun wata cuta ko kamuwa da ƙwayoyin cuta ba, duk da cewa an tabbatar da cutar dajin.
Jama'a sun taru a asibiti
Vatican News ta wallafa cewa kafin a yi masa tiyata, dimbin jama'a sun taru a wajen asibitin Gemelli na Rome, inda suka jira na tsawon sa'o'i domin yi wa masa fatan samun lafiya.
Wasu daga cikin jama'ar sun yi masa kirari da addu'o'i yayin da motarsa ta wuce, shi kuma ya riƙa daga musu hannu tare da murmushi ta tagar bayan motarsa da aka buɗe.

Source: Getty Images
Ma'aikatan asibitin sun tarbe shi, inda ɗaya daga cikinsu ya nuna masa tausayi, Fafaroma kuma ya amsa da murmushi.
A halin yanzu, ana ci gaba da gudanar da ƙarin gwaje-gwaje domin tabbatar da ko cutar ta bazu zuwa wasu sassan jikinsa ko kuma tana nan a huhun kawai.
Jacob Zuma ya kwanta a asibiti
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon shugaban ƙasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma, yana ci gaba da zama a asibiti, kamar yadda gidauniyarsa ta bayyana.
Gidauniyar Jacob G Zuma ta musanta wani rahoto da gidan talabijin na eNCA ya fitar cewa an sallami Zuma daga asibiti a daren Litinin a birnin Pietermaritzburg.
An garzaya da Zuma asibiti a cikin motar ɗaukar marasa lafiya ranar 6 ga Oktoba domin gudanar da abin da jam'iyyarsa ta bayyana a matsayin gwajin lafiya na yau da kullum.
Asali: Legit.ng

