Hisbah a Kano ta sasanta ma'aurata 3,079 a shekarar 2020 kadai
- Hukumar Hisbah ta bayyana cewa ta kokarta wajen sasanta ma'aurata 3.078 a 2020
- Hukumar ta kara da cewa ta tallafawa yara, mata, nakasassu da matafiya masu yawa
- Hakazalika hukumar ta bada gudunmawa wajen kwato yaran da a ka sace a jihar
Kwamandan Hisbah a jihar, Malam Ibrahim Dahiru ne ya bayyana hukumar Hisbah ta sasanta ma'aurata 3,079 a shekarar 2020 ya bayyana haka ne wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Dutse ranar Alhamis, Daily Nigerian ta ruwaito.
Mista Dahiru ya bayyana cewa sulhunta ma'aurata don tabbatar da zaman lafiya yana daya daga cikin hakkokin hukumar.
KU KARANTA: Babban hadari ne gwamnati ta ci bashin N9.8tn - Fitch Ratings
Ya ce hukumar ta kuma taimaka wajen sasanta rikice-rikicen da suka shafi ‘yan kasuwa 1,081, iyaye da yara, makwabta, da manoma da makiyaya.
Kwamandan ya kara da cewa hukumar ta kuma bayar da tallafin kudi ga marayu 101, marasa lafiya 18, matafiya 73, marassa galihu 506 da nakasassu 269 (PWDs).
A cewarsa, hukumar ta gabatar da kararraki guda hudu, fyade 149, haihuwar jarirai biyu, zubar da ciki hudu, luwadi bakwai da sata 66 a cikin wannan lokacin da yake jawabi.
Mista Dahiru ya ci gaba da cewa, hukumar ta Hisbah ta dawo da daliban Almajirai 701, da masu tabin hankali 12 da kuma ‘yan mata 21 da suka bar gida saboda auren dole da aka yi musu a garuruwansu da biranensu.
Bayan haka, ya ce hukumar ta kwato kananan yara 36 da suka bata sannan an samu rahoton laifuka 13 na fataucin yara.
Mista Dahiru ya bayyana cewa yayin da aka sasanta wasu shari'oin ba tare da kotu ba, wasu kuma an tura su kotu, 'yan sanda, kwamitoci da sauran hukumomin da abin ya shafa.
Kwamandan, wanda ya sake jaddada kudurin kwamitin na ci gaba da tabbatar da cewa mutane sun zauna cikin zaman lafiya da lumana, ya kara da cewa za ta kuma ci gaba da yaki da duk wasu nau’ikan dabi’u marasa kyau a jihar.
KU KARANTA: Gwamnatin tarayya tace ta shiryawa 'yan N-Power goma na arziki
A wani labarin, Gwamnatin Tarayya a ranar Talata ta ce tana niyyar tallafawa yara miliyan 10 da ba sa zuwa makaranta don cin gajiyar shirin ba da Ingantaccen ilimi ga Kowa (BESDA).
Karamin Ministan Ilimi, Hon. Chukwuemeka Nwajiuba ya bayyana hakan ne a ranar Talata a bikin kaddamar da bikin BESDA a garin Minna, babban birnin jihar Neja.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng