'An Yi Awa 9,' Yadda aka kai har Dare ana Shari'ar El Rufa'i a Kaduna

'An Yi Awa 9,' Yadda aka kai har Dare ana Shari'ar El Rufa'i a Kaduna

  • Kotu ta ɗage shari’ar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, kan zargin karkatar da kuɗin gwamnati zuwa ranakun 30 ga Nuwamba da 1 ga Disamba
  • Matakin ya biyo bayan da kotun ta yi watsi da ƙorafin lauyoyin El-Rufai kan shaidar wani jami’in DSS a fannin binciken na’urorin zamani
  • Hukumar ICPC na tuhumar tsohon gwamnan da laifuffuka tara da suka shafi zargin cin hanci da rashawa da kuma amfani da muƙami ba bisa ka'ida ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna – Babbar kotun jihar Kaduna ta ɗage shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, kan zargin karkatar da kuɗin gwamnati zuwa ranakun 30 ga Nuwamba da 1 ga Disamba, 2026.

Alƙalin da ke jagorantar shari’ar, Mai shari’a Darius Khobo, ya ɗauki wannan mataki ne domin ci gaba da yi wa wani jami’in hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) tambayoyi kan shaidar da ya bayar.

Kara karanta wannan

Tallafin Tinubu gida gida, dubban dalibai za su sake samun taimakon kudi

Lokacin zuwan El-Rufa'i kotu
Nasir El-Rufa'i da dan takarar ADC a Kaduna, Ashiru Kudan a harabar kotu. Hoto: ADC Vanguard
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan ta yi watsi da ƙorafin tawagar lauyoyin El-Rufai kan shaidar jami’in, Shegun Kayode, wanda aka gayyata bisa umarnin kotu domin bayar da shaida.

Korafin lauyan El-Rufa'i

Lauyan El-Rufai, Paul Erokoro, SAN, ya yi ƙorafi kan shaidar Kayode, yana mai cewa ba a ba tawagar tsaron takaitaccen bayanin shaidar ko takardar umarnin gayyatarsa ba.

Erokoro ya bayyana cewa rashin samun waɗannan takardu tun da wuri ya hana tawagar shirya yadda ya kamata domin yi wa shaidar tambayoyi da fahimtar tuhumar da ake son ta kare kanta a kai.

Sai dai lauyan hukumar ICPC, Ayodele Adedipe, ya ce rashin saka sunan shaidar da aka gayyata bisa umarnin kotu cikin jerin shaidun masu gabatar da ƙara ba ya nufin cewa ba za a iya karɓar shaidarsa ba.

A hukuncinsa, Mai shari’a Khobo ya tabbatar da cewa kotun ta bayar da umarnin gayyatar Kayode a ranar 30 ga Yuni, 2026.

Kara karanta wannan

Kwana ya ƙare: Tsohon Shugaban FRSC ta Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

Alƙalin ya ce za a iya kare haƙƙin El-Rufai na samun adalci ta hanyar ba lauyoyinsa damar yi wa shaidar tambayoyi domin tantance sahihancin bayanansa.

Abin da jami’in DSS ya ce a kotu

Tun da farko, Kayode ya shaida wa kotun cewa DSS ta gudanar da binciken fasaha kan bayanan sadarwa da wasu muryoyin da ake zargin suna da alaƙa da El-Rufai da wasu mutanen da ke kusa da shi.

Nasir El-Rufa'i a kotu
Lokacin da Nasir El-Rufa'i ya je kotu. Hoto: Uche Diala.
Source: Facebook

Ya ce hukumar ta gudanar da binciken ne bisa buƙatar ICPC da kuma amincewar darakta-janar na DSS.

A cewarsa, wani manhajar bincike ta musamman ta gano sadarwa tsakanin El-Rufai, ɗan'uwansa da wani mutum a tsakanin ranakun 25 zuwa 28 ga Oktoba, 2025.

Daga daga cikin mutanen El-Rufa'i, Uche Diala ya wallafa a Facebook cewa an shafe sa'o'i kimanin 9 ana shari'ar kafi daga ta zuwa wata mai kamawa.

Kotu ta yi watsti da bukatar El-Rufa'i

A wani labarin, mun ruwaito cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar domin hana hukumomi kwace kadarorinsa.

Kara karanta wannan

Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan buƙatar bada belin Nasir El Rufai

Mai shari'a Joyce Abdulmalik ce ta yanke hukuncin bayan ta bayyana cewa ƙarar ta zama amfani da tsarin shari'a ba bisa ƙa'ida ba.

Rahoto ya nuna cewa Malam Nasir El-Rufai ya shigar da ƙarar ne kan ICPC, EFCC, DSS da kuma babban lauyan gwamnatin tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng