'Yan damfara da sunan COVID-19 sun bayyana a birnin Abuja, FCTA

'Yan damfara da sunan COVID-19 sun bayyana a birnin Abuja, FCTA

- FCTA ta gano akwai faruwar damfara a wurare da dama a babban birnin tarayya da sunan aiwatar da bincike kan Korona

- Hukumar ta kuma bayyana cewa ba ta hannu wajen hukunta kowa kai tsaye a ko ina

- Sun kuma bayyana cewa kotun tafi-da-gidanka kadai ke da hakkin hukunta masu karya dokar Korona

Gwamnatin Babban Birnin Tarayya (FCTA) a ranar Alhamis ta sanar da mazauna cewa akwai 'yan damfara wadanda ake zargin suna zagayawa don karbar kudade daga masu shirya taro da sauran wurare a garin da sunan masu aiwatar da binciken COVID-19.

Shugaban Kafafen yada labarai da wayar da kai na rundunar tsaro kan COVID-19 ta FCT, Kwamared Ikharo Attah wanda ya yarda da faruwar irin wadannan munanan rahotanni, ya gargadi jama'a da su yi taka tsantsan.

Yayin da yake karyata jita-jitar da ake yadawa cewa mambobin rundunarsa na da hannu a aikata laifin, ya kuma bayyana cewa rundunar ‘yan sanda ta FCT ta fara farautar masu aikata laifin, The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA: Hisbah a Kano ta sasanta ma'aurata 3,079 a shekarar 2020 kada

'Yan damfara da sunan COVID-19 sun bayyana a birnin Abuja - FCTA
'Yan damfara da sunan COVID-19 sun bayyana a birnin Abuja - FCTA Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Ya kuma kara jaddada cewa kungiyar ta Shugaban kasa a kan COVID-19 ko kuma FCTA ba ta ba da izinin wani ya hukunta masu karya ka'idojin kiwon lafiyar ba.

Attah ya kara da cewa kotunan tafi-da-gidanka da gwamnati ta kafa ne kawai ke da ikon hukunta masu karya doka.

Ya shawarci mazauna yankin cewa duk wani gungun mutane da aka samu suna karbar kudi daga wasu jama’a ta kowacce fuska ya kamata a sanar da shi ga hukumomin da suka dace.

Kalaman nasa: “A zahiri muna aiki ne a kan tsarin aminci wanda Ministan Babban Birnin Tarayya, Malam Muhammad Musa Bello ya kafa tare a karkashin shugabancin Kwamishinan ’Yan sanda na Babban Birnin Tarayya, Bala Ciroma."

Ya kuma bayyana cewa idan suka kama masu aikata laifin suyi kuka da kansun domin doka zata yi aiki a kansu.

KU KARANTA: Kungiyar dattawan arewa ta yi Allah-wadai da kudurin korar Fulani

A wani labarin,

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel