Gwamnatin Tarayya tana sake ginawa, ta gyara hanyoyi 43 a manyan makarantu

Gwamnatin Tarayya tana sake ginawa, ta gyara hanyoyi 43 a manyan makarantu

- Gwamnatin tarayya ta bayyana irin ayyukan raya jami'o'i da take yi a fadin kasar

- Ministan ayyuka ya bayyana gwamnati na ginawa tare da gyara hanyoyi a jami'o'in kasar

- A wani taron bude aikin a Benue, ministan yace ana ayyukan ne don jin dadin dalibai da saukake dawainiyar karatunsu

Gwamnatin Tarayya, a jiya, ta ce tana kan ginawa tare da gyara hanyoyi sama da 43 a manyan makarantu a duk fadin kasar, The Sun ta ruwaito.

Da yake jawabi yayin mika aikin titin cikin gida mai nisan kilomita biyu wanda Gwamnatin Tarayya ta gyara tare da sake gina shi a Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya, Makurdi, Jihar Benue, Ministan ayyuka ya bayyana tasirin aikin.

Ya kara da cewa daliban suna sake nuna farin cikinsu dangane da halartar ajujuwa saboda an maido da wasu hanyoyi marasa kyau masu kyau.

KU KARANTA: ‘Yan Bindiga sun sace marayu 8 da wasu 3 a gidan marayu na Abuja

Gwamnatin Tarayya tana sake ginawa, ta gyara hanyoyi 43 a manyan makarantu
Gwamnatin Tarayya tana sake ginawa, ta gyara hanyoyi 43 a manyan makarantu Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

Ministan ya samu wakilci ne a wajen taron daga Kontrollan ayyuka na jihar ta Benue, Injiniya Charles Olasupo Oke.

"Ba za a iya jayayya ba cewa ingancin ilimi zai iya tasiri ta hanyar ingancin ababen more rayuwa da kuma yanayin ilmantarwa, kuma wadanda suke shakkar hakan su tambayi wasu daga ɗaliban makarantun da aikin ya shafa".

A cikin wata sanarwa, Mataimakin Shugaban Jami’ar Tarayya ta Aikin Gona dake Makurdi, Farfesa A.R. Kimbir, ya nuna godiya ga Gwamnatin Tarayya da Ministan game da aikin kawo hanyoyin.

Ya ce kaddamar da aikin titin ya zo ne kasa da watanni biyu bayan da aka samar da kamfanin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana mai karfin 8.25MW a cikin Makarantar.

KU KARANTA: Masu kiwon kaji na rokon Buhari kan shigo da masara da waken soya daga kasar waje

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin sakin dala miliyan 20 nan take, wanda Nijeriya ta yi alkawarin bayarwa a baya ga asusun ajiyar shirin ECOWAS na yaki da ta'addanci a fadin yankin, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban ya sanar da wannan umarni ne a yayin wata gabatarwa ga taron kara wa juna sani karo na 58 na Shugabannin kasashe da gwamnatocin ECOWAS, a Abuja, ranar Asabar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel