An Samu Akasi: Harshen Tinubu Ya Subuce, Ya Tafka Kuskure a tsakiyar Jama'a a Abuja

An Samu Akasi: Harshen Tinubu Ya Subuce, Ya Tafka Kuskure a tsakiyar Jama'a a Abuja

  • Shugaba Bola Tinubu ya yi subutar baki, ya kira kansa gwamna maimakon shugaban ƙasa yayin jawabi a wajen ƙaddamar da kamfen APC
  • Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan ƙoƙarin neman sake zaɓensa a wa’adi na biyu na shekaru huɗu
  • Kwamitin kamfen ya ƙunshi manyan ’yan APC da kuma wasu ’yan siyasa daga jam’iyyun adawa, ciki har da Nyesom Wike da Ademola Adeleke

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya yi subutar baki a jawabin da ya yi a wurin taron kaddamar da kwamitin yakin neman zabensa a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Shugaba Tinubu ua kira kansa gwamna maimkon shugaban kasa, lamarin da ya dan ja hankalin mahalarta taron.

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana jawabi a wurin taro a Abuja Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

The Cable ta ruwaito cewa Tinubu, wanda ke neman sake zaɓensa a wa’adi na biyu, ya faɗi hakan ne yayin da yake mika gaisuwa ga shugabannin jam’iyyar APC da mambobin kwamitin kamfen.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Tinubu ba zai iya zuwa kamfe a wasu jihohin Najeriya ba

Yadda Tinubu ya kira kansa da gwamna

Da yake magana, Tinubu ya ce:

“Manyan shugabannin jam’iyyarmu, dukkan mambobin jam’iyya da kwamitin kamfen shugaban ƙasa, na ga abokina a nan wanda dole ne in gode masa.
"Na gaba kuma shi ne bayyana darajar darakta-janar na kwamitin yakin qneman zaben shugaban ƙasa, wanda za mu dawo da Gwamna Bola Tinubu karo na biyu.”

A yayin jawabin, shugaban ya bayyana kamar ya yi kuskuren kiran kansa gwamna maimakon shugaban ƙasa, yayin da yake magana kan burinsa na sake samun wa’adin mulki na shekaru huɗu.

APC ta kaddamar da kwamitin kamfe

APC ta ƙaddamar da kwamitin yakin neman zabe yayin da jam’iyyar ke ƙara shirye-shiryen tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na 2027, wanda aka tsara gudanarwa a ranar 16 ga Janairu, 2027.

Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, su ne shugaban kwamitin kamfen APC da mataimakinsa yayin da Sanata Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan Zamfara, ke riƙe da muƙamin darakta-janar.

Kara karanta wannan

Magana ta fito daga bakin minista, an ji adadin shekarun da Tinubu ke buƙata a kan mulki

Kwamitin yakin neman zaben ya ƙunshi shugabannin jam’iyyar APC, jami’an gwamnati da kuma ’yan siyasa daga sassa daban-daban na ƙasar.

Daga cikin mambobinta akwai Nentawe Yilwatda, shugaban jam’iyyar APC na ƙasa; Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio; Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas; da Femi Gbajabiamila, shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa.

Kwamitin ya kuma ƙunshi ’yan siyasa daga wasu jam’iyyun, ciki har da Nyesom Wike, ministan Abuja kuma mamba a jam’iyyar PDP, da Ademola Adeleke, gwamnan jihar Osun kuma mamba a jam’iyyar Accord.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262