Minista Ya Ballo Ruwa a gaban Kasashen Duniya, Ya Yi Maganar da ka Iya Juyo Wa kan Tinubu
- Ministan Kuɗi, Taiwo Oyedele, ya ce a halin da mutne je ciki, bai kamata gwamnati ta ƙara haraji ko nauyin haraji kan masu ƙaramin ƙarfi ba
- Ya buƙaci gwamnatoci su inganta tattara kuɗaɗen shiga tare da rage almubazzaranci maimakon ƙara wa 'yan ƙasa da 'yan kasuwa nauyin kuɗi
- Oyedele ya ce ya kamata a yi amfani da rance wajen samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziki ta yadda kowa zai amfana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ministan Kuɗi kuma mai kula da tattalin arzikin Najeriya, Taiwo Oyedele, ya yi kalamai kan haraji wadanda za su iya hawa kan gwamnatin Tinubu.
Oyedele ya bayyana cewa a halin da ake ciki yanzu, bai dace gwamnatoci su ƙaƙaba sababbin haraji ko ƙara nauyin haraji kan talakawa da ɓangarorin tattalin arziki ba.

Kara karanta wannan
Magana ta fito daga bakin minista, an ji adadin shekarun da Tinubu ke buƙata a kan mulki

Source: Facebook
Daily Trust ta ce Oyedele ya bayyana hakan ne a gefen taron shekara-shekara na 2026 na Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya, wanda ake gudanarwa a Bangkok, babban birnin Thailand.
Gwamnatin Shugaba Tinubu ya gudanar da gyara tare da kirkiro sababbin dokokin haraji, wadanda ake zargin sun jawo matsalolin rayuwa da yan kasa.
Ministan Tinubu ya yi jawabi jan haraji
A cewarsa, ya kamata gwamnatoci su daidaita hanyoyin tattara kuɗaɗen shiga da buƙatar kare al'ummomin da ke cikin mawuyacin hali daga ƙarin matsin tattalin arziki.
“Wannan ba lokacin da ya dace a ƙaƙaba sababbin haraji ko ƙara nauyin haraji ba ne, musamman kan masu talakawa da kuma ɓangarorin tattalin arzikin da ke samar da kayayyaki da ayyuka,” in ji Oyedele.
Ministan ya ce ya kamata gwamnatoci su duba hanyoyin rage kashe kuɗi da kuma inganta tattara kuɗaɗen shiga, ba tare da ƙara wa 'yan ƙasa da 'yan kasuwa nauyi ba.
Ya ce:
“Matakan da za a ɗauka, kamar yadda kuka tambaya, za su fara ne da kowace ƙasa ta duba cikin harkokinta domin gano wuraren da za ta rage kashe kuɗi da kuma inganta tattara kuɗaɗen shiga."
Rance da bunƙasa tattalin arziki
Oyedele ya ce ciwo bashi na ci gaba da kasancewa wani muhimmin mataki wajen bunƙasa tattalin arziki, amma ya jaddada cewa ya kamata a yi amfani da kuɗin wajen samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arzikin da kowa zai amfana da shi.

Source: Twitter
Ya kuma ce ya kamata a karkatar da kuɗaɗen gwamnati zuwa muhimman ayyuka kamar kiwon lafiya da ilimi, yayin da za a iya amfani da jarin kamfanoni masu zaman kansu wajen biyan sauran buƙatun zuba jari, cewar rahoton Vanguard.
Oyedele ya soki shirin dawo da tallafi
Kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta ce ba za ta dawo da tallafin man fetur ba, tana mai cewa zai iya lakume sama da Naira tiriliyan 20 a shekara
Ministan Kuɗi, Taiwo Oyedele, ya ce dawo da tallafin na iya lalata darajar Naira zuwa kusan N3,000 kan Dala guda cikin watanni.
Asali: Legit.ng
