Tawagar Turawa Ta Tona Asirin Badakalar da aka Yi a Zabukan Jihohin Najeriya

Tawagar Turawa Ta Tona Asirin Badakalar da aka Yi a Zabukan Jihohin Najeriya

  • Wata ƙungiyar masu sa ido kan zaɓe ta Tarayyar Turai ta bayyana cewa sayen ƙuri’u ya yi kamari a zaɓen gwamnonin jihohin Ekiti da Osun na 2026
  • Ƙungiyar ta ce kashi 77 na abubuwan da ta tantance da suka shafi maguɗin zaɓe sun shafi sayen ƙuri’u, yayin da wakilan jam’iyyun siyasa suka taka rawa sosai
  • Masu sa ido sun kuma yi gargaɗin cewa rashin hukunta waɗanda aka samu da sayen ƙuri’u na ƙara ƙarfafa wannan aika-aika, tare da kira ga INEC ta dauki mataki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma ƙwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Ƙungiyar masu sa ido kan zaɓe ta Tarayyar Turai ta bayyana cewa sayen ƙuri’u ya yi kamari a zaɓen gwamnonin jihohin Ekiti da Osun da aka gudanar a watan Yuni da Agustan 2026.

Kara karanta wannan

Kowa ya bi: An gano motar kamfen PDP da hoton Tinubu, bidiyon ya jawo magana

Farfesa Bolade Eyinla ne ya bayyana hakan yayin gabatar da rahoton sa ido kan zaɓukan a Abuja ranar Talata.

Wajen zaben Osun da tambarin EU
Wajen da aka yi zabe a Osun da tambarin EU. Hoto: INEC Nigeria|Getty Images
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Eyinla ya ce masu zaɓe sun karɓi kuɗi har N50,000 domin sayar da ƙuri’unsu, yana mai gargaɗin cewa lamarin na barazana ga sahihancin zaɓe da ‘yancin ɗan ƙasa na zaɓar wanda yake so.

Ya ce:

“Annobar sayen ƙuri’u tana ƙara yaɗuwa kamar cuta. Idan ba mu ɗauki mataki ba, mutuncin ƙuri’a da ‘yancin zaɓen wanda mutum yake so za su ci gaba da fuskantar barazana mai tsanani.”

Yadda aka saye ƙuri’u

Eyinla ya bayyana cewa sayen ƙuri’u ya kasance cikin tsari na makirci kuma duk da haka ba a hukunta masu aikata laifin yadda ya kamata.

Ya ce bayanan da suka tattara sun nuna cewa kashi 77 cikin 100 na abubuwa 84 da suka tantance sun shafi sayen ƙuri’u, yayin da wakilan jam’iyyun siyasa suka kasance manyan masu aikata irin wannan laifi a akalla kashi 90 cikin 100 na lamuran.

A jihar Osun kuwa, ya ce kashi 69 cikin 100 na abubuwan da aka tantance sun shafi sayen ƙuri’u.

Kara karanta wannan

Magana ta fito daga bakin minista, an ji adadin shekarun da Tinubu ke buƙata a kan mulki

Ya ƙara da cewa har yanzu ba a samu rahotannin kama waɗanda ake zargi, gudanar da bincike ko gurfanar da su a gaban kotu ba, duk da girman matsalar da aka gani a zaɓukan biyu.

Eyinla ya bayyana yadda ake gudanar da lamarin, inda ya ce mai zaɓe kan nuna alamar zaɓensa a takardar ƙuri’a, sannan ya nuna wa masu sa ido ko wakilan da ke biyan kuɗi domin tabbatar da cewa ya zaɓi ɗan takarar da aka buƙata.

Ya kara da cewa bayan tabbatar da ya zabi wanda ake so ne ake ba shi kuɗin da aka yi yarjejeniya a kai.

Kiran kungiyar ga INEC

Ƙungiyar ta kuma yi kira ga hukumar INEC da ta riƙa wallafa sakamakon zaɓe daga matakin gundumomi domin ƙara gaskiya da sahihanci a tsarin zaɓe.

Eyinla ya ce yawancin matsalolin da suka shafi maguɗin zaɓe suna faruwa ne a matakin gundumomi, don haka wallafa sakamakon daga wannan mataki zai taimaka wajen sa ido kan yadda ake gudanar da zaɓe.

Wajen tattara sakamakon zabe
Wajen da INEC ta tattara sakamakn zaben Osun. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

The Guardin ta wallafa cewa ya ce idan hukumar za ta iya ɗaura sakamakon rumfunan zaɓe a intanet, to ya kamata ta iya wallafa sakamakon gundumomi ma.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi sabon bidiyo ya kira Tinubu da 'Bola' duk da APC ta yi gargadi

Kiran INEC ga 'yan takarar 2027

A wani labarin, mun ruwaito cewa INEC ta ba jam’iyyun siyasa wa’adin ranar 24 ga Oktoba domin sanar da ita korafe-korafen cire sunayen ‘yan takararsu daga jerin waɗanda za su fafata a zaɓen gwamnonin 2027.

Hukumar ta ce wa’adin ya yi daidai da Sashe na 32(2) na Dokar Zaɓe ta 2026, wanda ya bai wa jam’iyyun kwana 14 domin sanar da ita idan suna ganin an cire sunayen ‘yan takararsu bisa kuskure.

Daga cikin waɗanda ba a saka sunayensu a jerin ba akwai ‘yan takarar gwamnan Gombe da Ogun na PDP, Farfesa Isa Ali Pantami da Oladipupo Adebutu, da kuma Aminu Gwarzo na NDC a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng