NCC Ta Bullo da Wani Tsari, Mutane na Iya Asarar Wayoyin da Suka Saya da Kudinsu a Najeriya

NCC Ta Bullo da Wani Tsari, Mutane na Iya Asarar Wayoyin da Suka Saya da Kudinsu a Najeriya

  • Hukumar NCC ta fara tantance sahihancin na'urorin da ke amfani da katin SIM kamar wayoyin hannu domin gano na jabu da waɗanda ba su cika ƙa'idoji ba
  • Hukumar ta ce matakin zai taimaka wajen inganta ayyukan sadarwa da kuma kare masu amfani da na'urori marasa inganci
  • NCC ta buƙaci masu sayen waya, kwamfutar hannu, modem, POS da sauran na'urorin da ke amfani da SIM su tabbatar ta amince da su kafin saye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria – Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta ce ta fara tantance sahihancin na'urorin da ke amfani da layin SIM da suka hada da wayoyin hannu da kwamfutoci domin gano tare da hana amfani da na jabu a kasar nan.

Hukumar ta bayyana shirinta na toshe irin wadannana na'urori kamar wayoyi da kwamfutoci, waɗanda aka kwaikwaya da kuma waɗanda ba su cika ƙa'idoji ba shiga hanyoyin sadarwa.

Kara karanta wannan

An kwance wa Kwankwaso zani a kasuwa da NNPP ta fadi shirinta kan babban zaben 2027

Hukumar NCC.
Hedkwatar hukumar kula da harkokin sadarwa ta NCC Hoto: NCCNigeria
Source: Twitter

The Cable ta ruwaito cewa Daraktan kula da ƙa'idojin fasaha da ingancin hanyoyin sadarwa na NCC, Edoyemi Ogoh, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin wani taron manema labarai.

Amincewa da nau'in na'ura wani tsari ne na doka da NCC ke bi wajen tabbatar da cewa na'urorin sadarwa sun cika ƙa'idojin fasaha da aka shimfiɗa kafin a sayar da su ko amfani da su a Najeriya.

Dalilin NCC na daukar mataki

Ogoh ya ce sabon tsarin bin ƙa'idojin zai ƙarfafa sa ido kan wayoyin da ake shigo da su Najeriya, sayarwa da kuma amfani da su a ƙasar.

Ya bayyana cewa tsarin zai bai wa hukumar damar tantance su bisa ƙa'idojin amincewa da nau'in na'ura, inganta ayyukan hanyoyin sadarwa da kuma kare masu amfani da su da ba su cika ƙa'idojin fasaha da ake buƙata ba.

“Muna so mu tabbatar da cewa an yi rajistar na'urorin da mutane ke amdani da su a halin yanzu yadda ya kamata, sannan za a tantance tare da tabbatar da sahihancin wadanda da za a ci gaba da shigo da su Najeriya."

Kara karanta wannan

2027: INEC ta kawo mafita ga 'yan takarar da aka cire sunayensu

“Wannan zai samar da ingantacciyar hanya ta gano wadanda ba su cika ƙa'idoji ba, waɗanda aka kwaikwaya ko kuma na jabu, tare da hana su haɗuwa da hanyoyin sadarwarmu," in ji shi.

NCC za ta hada kai da Kwastam

Ya ce hukumar NCC za ta ci gaba da aiki tare da Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) da sauran masu ruwa da tsaki a dukkan matakan samarwa da rarraba wayoyi, kwamfutoci da zauran na'urori domin taimakawa wajen aiwatar da tsarin.

A cewar Ogoh, sashe na 132(2) na Dokar Sadarwa ta Najeriya ta 2003 ya tanadi cewa duk wata na'urar sadarwa da aka yi niyyar sayarwa ko amfani da ita a Najeriya dole ne ta samu amincewar nau'in na'ura daga hukumar.

Wayoyi.
Wayoyin hannu a turken kamfanin sadarwa a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

NCC ta ja hankalin masu sayen wayoyi

Daraktan ya shawarci masu amfani da wayoyin hannu, kwamfutoci, modem da su tabbatar da sahihancin amincewar NCC kafin subsaye su

Ogoh ya ce ya kamata masu saye su tambayi dillalai ko wayar hannu, kwamfutar hannu, modem, na'urar karɓar kuɗi ta POS ko wata na'urar da ke amfani da katin SIM ta samu amincewar NCC.

Kara karanta wannan

Pantami ya tara manyan lauyoyi sun tunkari INEC kan cire sunan shi

TikTok ya daina aiki a Arewa?

Kun ji cewa kamfanin sada zumunta na TikTok ya musanta rade-radin cewa ya daina aiki ko takait amfani da manhajarsa a Arewacin Najeriya.

Kamfanin ya ce yana tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin magance matsalolin shiga manhajar TikTok da aka ruwaito yan Arewa na fama da shi

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262